Nijar: Wata cutar dabbobi na saurin hallaka jakuna a karkara

A yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar hankulan likitotin dabbobi da masu jakuna sun tashi haikan a sakamakon bullar wata cuta da ke saurin hallaka jakuna.

A cewar likitotin, hatta dawakai ba su tsira daga kamuwa da cutar ba, sai dai su ba ta saurin kashe su kamar yadda take tasiri a kan jakuna. Tuni dai  likitotin dabbobi suka yi ca a kan cutar ganin yadda jaki ke da mahimmanci ga mazauna karkara.

Daga dan karamin tari irin na kamun mura tare da zubda majina gami da hajijiya ko juya sune ire-iren alamomin da masu jakai suka ankara na tabbatuwar cutar a kan jakuna kamar yadda Malam Buniya Minu ya shedar.

"Jakina sai da ya yi kwana 15 a kwance, da farko na yi tsammanin majina ce, na fara yi masa magani na gargajiya, amma bai samu sauki ba. Dole sai da na hada da likita wanda ya yi ta zuwa yana yi masa allura tsawon kwana uku. Ni dai nawa ya tsira, amma har yanzu bai yana tafiya a karkace kamar ya sha giya."

Dakta Isaka Abdullai shi ne jagoran hukumar kula da lafiyar dabbobi ya yi karin haske game da bullar cutar mai saurin hallaka jakuna.

Rahotanni masu dangantaka

"Na zagaya cikin jiha, mun dauko jinin jakuna mun aika Yamai. Nan da wasu kwanaki za a kawo mana magunguna da za mu je mu ba wa dabbobin da suka kamu da wannan cuta da ke kama jakai da dawaki. Dawakin dai ba sam mutuwa amma mafi jakai ne ke mutuwa."

Matakan kariya don hana cutar yaduwa

Bai kamata a hada mai ciwo da mai lafiya wurin shan ruwa guda ba

Da dama dai shedun gani da ido kan cutar da suka hada da manoman karkara a irin wannan lokaci na tattara amfanin gona kama daga gero zuwa harawa da ma karmami sun yi matukar nuna damua game da cutar ai saurin kashe jakuna.

Hakikan jaki na da muhimmanci ga al'umma musamman ta karkara wanda wani lokaci ke kasancewa jigo wajen rikon iyali sakamakon rawar da yake takawa a aikace-aikacen neman na sakawa a bakin salati.

Dakta Isaka Abdullai ya bayyana matakan da suka dauka na dakile cutar.

"Lokacin da ciwon ya bulla mun ja hankalin mutane duk wanda ciwon ya kama dabbarsa, bai kamata dabbar ta sha ruwa tare da 'yan uwanta ba, ya kamata a ware shi. Wadanda kuma suka mutu bai kamata a barsu a yashe ba, a gina rami a sa su ciki, in an yi haka ciwon ba zai yadu ba."

A 'yan shekarun nan dai hawan farashin jaki gami da taunarsa ya sa rikonsa sai wane da wane.

Bayanai masu kama