1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa za su hade wa gwamnati kai

Salissou Boukari
September 2, 2020

A wani mataki na neman tilastawa gwamnati mai ci gudanar da zabuka da ma burin ganin mulkin kasar ya sauya hannu, jam'iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya.

https://p.dw.com/p/3hv8L
Hama Amadou
Babban jagoran adawar Jamhuriyar Nijar Hama AmadouHoto: Imago/W. Prange

Dubban magoya bayan 'yan adawar ne dai suka hallara a Yamai babban birnin kasar ta Nijar, domin nuna goyon bayansu ga gamayyar adawar da aka yi wa lakabi da "Cap 2021-2021." Kimanin jam'iyyun siyasa 20 ne dai suka hadu a karkashin inuwar wannan gamayya, domin gama karfin wajen tunkarar zabukan kasar masu zuwa.

 

Karin Bayani: Zaben Nijar: CENI ta gana da jam'iyyu

 

Daga cikin shugabannin jam'iyyun adawa da ke kan gaba wajen wannan kokawa, akwai tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane shugaban jam'iyyar RDR canji da Hama Amadou shugaban jam'iyyar Lumana Afirka da Ibrahim Yakouba na jam'iyyar Kishin Kasa da Ladan Tchana na Ain-Amin da Malam Mamane Sani Adamou na ORDN Tarmamuwa da dai sauran jam'iyyu da dama, har ma na bangaran 'yan ba ruwanmu.

Mahamane Ousman Ex-Präsident Niger
Tsohon shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar Mahamane OusmanHoto: DW/M. Kanta

Zauran taro dai na Palais de Sport ya cika mail da jama'a inda magoya bayan dukannin wadannan jam'iyyu sanye cikin tufafin jam'iyyunsu ko rike da kyallaye na shaidar jam'iyya domin kawo goyon bayansu ga wanen babbar haduwa ta tunkarar zabukan kasar masu zuwa. Suma dai matasa ba'a bars a baya ba, domin kuwa a cewar wata matashiya Jamila Boubakar su dai kawai canji suke nema mai albarka.

A halin yanzu dai nan da 'yan kwanaki masu zuwa lamura za su sauya a fagen siyasar ta Nijar, inda za a gudanar da  zaben kananan hukumomi a Disamba  kuma akwai yiwuwar zamun karin jam'iyyun da za su ruga da kudu wajen 'yan adawar domin shiga wannan kokowa ta ganin an yi zabukan na Nijar cikin haske da kwanciyar hankali. Ko da yake daga bangaren masu mulki sun ce ko kada wasa yunkarı bai kayar da gaban doki.