1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Nijar na zargin hukumar zabe CENI

Salissou Boukari AH
July 27, 2020

Bayan kwashe dogon lokaci ana yin tankiya tsakanin 'yan siyasar Nijar a game da ranaikun zabe na kananan hukumomi, a karhe hukumar zabe CENI ta ce za a yi zaben kananan hukumomin a Disamba.

https://p.dw.com/p/3fygG
Niger Niamey Präsidentschaftswahl Plakat Wahlkommission CENI
Hoto: DW/K. Gänsler

Hukumar zabe ta Jamhuriyar Nijar ta bayyana ranar 13 ga watan Disamban da ke tafe a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda mafi yawan jam'iyyun siyasar har ma da na adawa suka bukata. Sai dai 'yan adawar na zargin cewar  hukumar ta CENI ta hada baki da masu mulkin kasar don gudanar da magudi a yayin manyan zabukan da ke tafe. An dai kwashe tsawon lokaci kafin zaben ana ta yin gardama tsakanin 'yan adawar da hukumar kafin daga bisani ta bayyana ranaikun zaben.

Zargin magudi daga 'yan adawar na Nijar a kan hukumar zabe

Ibrahim Yacoubou daya daga cikin shugabannin 'yan adawa na Nijar
Ibrahim Yacoubou daya daga cikin shugabannin 'yan adawa na NijarHoto: DW/N. Amadou

Shi dai ‘yan magana ke cewa tun ranar gini ranar zane, domin kuwa tun ranar da aka kafa hukumar zaben kasar ta Nijar mai zaman kanta CENI, mutane da dama musamman ma bangaran ‘yan adawa suka ce sun rufe idanu ba su kyawan makanta ba. Domin suna ganin yadda bangaran gwamnati ya yi ruwa ya yi tsaki na ganin an dauki wasu a cikin wannan hukumar ta zabe abin da ke nuni da cewar akwai alamun magudi. Kuma tun wannan lokaci ake ci gaba da yin takun saka har ma na baya-bayan nan ‘yan adawar suka bankado wasu abubuwan na shirin magudin.

Martanin hukumar zaben ta Nijar game da zargin 'yan adawar

Niger Wahllokal in Niamey
Hoto: DW/A. Amadou

Duk da zarge-zarge da ake yi wa hukumar zaben ta Nijar CENI a karon farko ta fito ta yi magana, inda ta ce ya kyautu ‘yan Nijar su lura da yadda wannan hukuma ke tafiyar da ayyukan ta cikin tsanaki domin ba ta da wata mugunyar aniya ga wadannan zabuka da ke tafe. Docta Aladoua Amada, mataimakin shugaban hukumar zaben kasar ta Nijar CENI ya ce sun dau matakai na kiyaye magudi don haka 'yan adawar su kwantar da hankulan su. Tun farko dai a cewar su hukumar zaben ta Nijar ta ce ta tuntubi hukumar OIF ta kasashe masu magana da harshen Faransanci, da ma kungiyar ECOWAS da cewar da su turo kwararru domin duba girgam ko jerin sunayan masu zaben na Nijar domin tantance sahihancin shi.