1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Nijar sun zargi gwamnati

Mahaman Kanta LMJ
June 16, 2020

Shugabannin gun-gun jam'iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar, sun zargi mahukuntan kasar na yanzu da cin zarafi da take hakki da kuma nuna wariya.

https://p.dw.com/p/3dsdZ
Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar NijarHoto: Presidence RDC/G. Kusema

Dambarwar siyasa iri-iri ce dai ke tasowa a Jamhuriyar ta Nijar, kasa da shekara guda gabanin babban zaben kasar na gama gari. 'Yan adawar dai sun kira taron manema labaran ne bayan da hukumar zaben kasar CENI ta kammala rijistar masu zabe, ba tare da sanya sunan 'yan kasar da ke zaune a kasashen ketare ba.

A yayin taron da suka gudanar dai, 'yan adawar sun zargi gwamnatin Nijar din karkashin jagorancin Shugaba Issoufou Mahamadou da nuna fin karfi da cin zarafin masu fafutuka da 'yan adawa. A sanarwar bayan taron nasu, sun bayyana cewa cikin shekaru sama da 50 da Jamhuriyar ta Nijar ta samu 'yancin kai, babu wata gwamnati da ta yi mulkin kama karya da danniya kamar gwamnati mai ci yanzu ta Shugaba Issoufou da ta kwshe tsawon shekaru tara a kan madafun iko.

Sun kara da cewa gwamnatin na nuna wariya ga 'yan adawa ta yadda ba ta sanya su a harkokin gudanar da mulkin, inda suka yi zargin cewa mulki ne kawai irin na 'yan kama karya. 'Yan adawar dai sun sanya kafa sun yi fatali da batun yin taron sasantawa kan dokokin zabe, inda suka yi zargin cewa gwamnatin na son yin magudi ne shi ya sanya suke cewa za su kira taron sasantawar. Sai dai a nasu bangaren, 'ya'yan jam'iyyar adawa sun yi fatali da wannan zargin, suna masu cewa tun da farko sai da bangaren adawar ya amince da dokokin zaben.