1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Takaitaccen tarihin Sarauniya Njinga Mbande

Yusuf Bala Nayaya ZMA
July 10, 2018

Jami'ar diflomasiyya kuma shugabar sojoji a karni na 17, Njinga Mbande ta yi duk mai yiwuwa wajen yakar Turawan mulkin mallaka daga kasar Portugal.

https://p.dw.com/p/2uFGt
African Roots Njinga Mbande
Hoto: Comic Republic

Rayuwa: 

Ta rayu a kasar da a yau ake kira Angola. Bisa kiyasi an haife ta a shekarar 1583 a yankin Ndongo, ta mutu a ranar 17 ga watan Disambar 1663 a yankin Matamba.

 

Fagen da ta yi fice: 

Ta karar da rayuwarta wajen yaki da Turawan mulkin mallaka daga Portugal ta hanyar amfani da kwarewarta a fannin diflomasiyya da ma aikin soja a karni na 17 a yankin da ke a karkashin Angola a wannan lokaci.

 

Sukar da ake mata: 

Halayyar rashin imaninta da ya hada da kisan dan dan uwanta a kokarinta na samun mulkin Ndongo da harkokin cinikin bayi da cimma huldar kasuwanci ta tura bayi ga Turawan Potugal da na Holand uwa uba ga zarginta da halayyar cin naman mutane wato koyi da halayyar kawayenta mayakan Imbangala.

 

Njinga ba ta mika wuya:

A shekarar 1622 mai sarauta Ngola Mbande wato dan uwan Njinga ya aikata zuwa Luanda don kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yankin Ndongo da gwamnan Portugal. An mika mata darduma don ta zauna maimakon kujera abin da ke nuna cewa an kaskantar da ita, nan Njinga ta nemi daya daga cikin bayinta ya durkusa kan gwiwarsa ta zauna a bayansa tamkar kujera, aka ci gaba da kulla yarjejeniya da ita ba tare da jin ta koma baya ba.

Njinga Mbande: Sarauniyar al'ummar Mbundu

Njinga mai ilimi: 

Ta lakanci harsuna da dama na al'ummarsu haka nan ta iya harshen Turawan Portugal, tana da ilimi don haka hatta rubutu na tattaunawar da ake da ita da Turawan da kanta take rubutawa. Samun alaka da 'yan mishan tun da fari da ma Turawan Portugal 'yan kasuwa, sun taimaka mata a wannan fanni. Tana da gogewa ta diflomasiyya ga sanin harkokin soja duk sun taimaka mata a alaka da Turawan Portugal da Holand.

 

Njinga gwarzuwa: 

Njinga an gabatar da ita a fagen yaki a madadin babanta Sarki Kiluanji, a lokacin mulkinta takan yi yaki a matsayin soja abin da ke nunata a matsayin mace mai kamar maza.

A cewar wasu masana tarihi Njinga daga baya ta ki karbar sarauta a matsayin sarauniya face a kirata da sarki, a zamantakewa ita namiji ce, inda ta tara maza a matsayin kuyangi suna sanya kaya tamkar mata.

 

Wadanda suka yi hidima wajen hada labarin: Carla Fernandes da Gwendolin Hilse. Wannan bangare ne na shiri na musamman Tushen Afirka "African Roots", shirin hadin gwiwa tsakanin tashar DW da Gidauniyar Gerda Henkel.