1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nukiliya: Putin ya zanta da Kim Jong Un

Ahmed Salisu
April 25, 2019

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya yi wani zama na musamman da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a yau Alhamis kan shirin nukiliyar Arewa din.

https://p.dw.com/p/3HNpe
Russland Wladiwostok Treffen Putin und Kim
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Zemlianichenko

A jawabinsa lokacin bude taron wanda ya gudana a wata jami'a da ke tsibirin nan na Russky, Shugaba Putin ya ce ya na da tabbacin cewar ziyarar ta Kim da ma zantawar tasu za ta taimaka wajen gano bakin zaren warware takaddamar da ake fuskanta tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu.

A nasa bangaren, Shugaba Kim ya ce ya na da tabbacin cewar tattaunawarsa da Putin za ta haifar da mai idanuna musamman da yake hankalin duniya yanzu ya karkata kan yankin na Koriya da irin takun sakar da ake fuskanta a wajen.

Ziyarar ta shugaban na Koriya ta Arewa a Rasha dai na zuwa ne watanni biyu bayan da aka gaza yin zama makamancin wannan tsakanin Kim din da shugaban Amirka Donald Trump saboda gaza fahimtar juna dangane da takunkumin da Amirka din ta kakabawa Arewa.