1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nuna Kyama ga ma'aikatan lafiya kan Ebola

Lateefa Mustapha Ja'afarOctober 28, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kyama da ake nunawa ga ma'aikatan lafiyar da suka kula da masu dauke da cutar nan mai saurin kisa wato Ebola.

https://p.dw.com/p/1DdKS
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Baba Ahmed

Wannan batu dai ya fito ne daga bakin kakakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya wato Stephane Dujarric, inda ya ce ma'aikatan lafiyar da suka dawo daga Laberiya ko Gini ko kuma Saliyo ma'aikata ne da suka sadaukar da rayuwarsu domin ceto rayukan al'umma.

Majalisar ta Dinkin Duniya na yin wannan gargadi ne a daidai lokacin da Amirka ta dauki matakin killace sojojinta da suka dawo daga kasashen da ke fama da cutar Ebola na yankin Afirka ta yamma da ta tura domin su taimaka wajen dakile cutar.

Rahotanni sun bayyana cewa an killace dakarun Amirkan masu yawa inda za su ci gaba da zama na tsahon kwanaki 21cikinsun kuwa har da shugaban tawagar sojojin da ya sanya idanu kan yadda suka gudanar da aikin bada agaji a kasashen Afirka ta Yamman majo janar Darryl Williams.