1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi da Kirista sai sun hada kai a yaki da 'yan ta'adda

Yusuf BalaJuly 26, 2015

Obama ya bukaci matasa su zama masu kwazo dan cimma ɓurinsu ba wai sai sun tsallaka ruwa ba zuwa wasu ƙasashe kafin cikar ɓuri.

https://p.dw.com/p/1G4p4
Kenia USA Rede Präsident Barack Obama in Nairobi
Shugaba Obama a KenyaHoto: Reuters/J. Ernst

Da yake jawabinsa na ban kwana da matasa a ƙasar Kenya bayan kammala ziyarar kwanaki biyu a ƙasar shugaba Obama ya ce babu wata al'umma da za ta samu ci gaba ba tare da samar wa yara da mata ilimi ba.A ziyararsa mai cike da ɗinbin tarihi a ƙasar Kenya wacce ke kallonsa a matsayin ɗanta shugaba Obama ya ce dole ne a haɗa karfi da ƙarfe Musulmi da Kirista wajen yaƙi da masu kakkausan kishin addini da ke ayyukan ta'addanci.Wani abu da al'ummar wannan ƙasa suka ɗade suna mafarki bayan sun dade a shafukan intanet suna yaɗa bayanai cike da ɓurin ganin Obama ya ziyarcesu a matsayin shugaban ƙasar ta Amirka, a ranar Lahadin nan mafakirsu ya zama gaskiyya inda ya tattauna da su kai tsaye.

Obama dai ya kafa tarihi da zama shugaban ƙasar Amirka mai ci na farko da ya ziyarci wannan ƙasa ta Kenya. A jawabin nasa na ranar Lahadin da ya maida hankali kan dangantakar ƙasar ta Amirka da Kenya Obama ya buƙaci matasa su zama masu kwazo dan cimma ɓurinsu ba wai sai sun tsallaka ruwa ba zuwa wasu ƙasashe kafin cika ɓurinsu.

Rabonsa da ziyarartar Kenya tun a shekarar 2006 lokacin yana matsayin sanata a Amirka.