1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya ce ana aiki tukuru don murkushe kungiyar IS

Mohammad Nasiru AwalNovember 16, 2015

Manyan kasashen duniya sun lashi takobin kawar da ayyukan ta'addanci a duniya, biyo bayan hare-haren ta'addanci a kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/1H6qb
Barack Obama Pressekonferenz G20 Gipfel Antalya
Hoto: DW/B. Riegert

Shugaban Amirka Barack Obama ya ce ba za a sake dubarar yakin da ake yi da kungiyar IS ba, inda ya kara da cewa girke sojojin kasa na Amirka don yakar kungiyar zai zama kuskure. Shugaban na Amirka ya yi wadannan kalamai ne a karshen taron kolin kunghiyar G-20 a birnin Antalya na kasar Turkiyya. Ya ce za a hada karfi da karfe don murkushe kungiyar.

"Muna aiki kut da kut da kasar Faransa a daidai lokacin da take farautar wadanda ake zargi da hannu a hare-haren birnin Paris. Kanmu a hade yake don yakar wannan barazana. IS fuska ce ta shaidan. Burinmu shi ne kawar da wannan muguwar kungiyar 'yan ta'adda mai aikata ta'asa."

Shugabannin kasashen kungiyar ta G-20 sun sha alwashin daukar duk matakan da suka wajaba don maganin ayyukan ta'addanci da suka ce su ne manyan kalubalen wannan zamani.