1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya gana da shugabannin Jamus da Faransa da Italiya

May 31, 2012

Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da shugabar gwamnatin Jamus da shugaban Faransa da kuma Priyiministan Italiya kan batun tattalin arziƙin Turai.

https://p.dw.com/p/1559Y
Frankreichs Praesident Francois Hollande (v.l.), US-Praesident Barack Obama und Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) posieren am Samstag (19.05.12) in Camp David (USA) beim Familienfoto des G-8-Gipfels. Die Fuehrer der acht grossen Industriestaaten beraten auf dem Landsitz des amerikanischen Praesidenten die Wirtschafts- und Finanzpolitik, die Entwicklung des Klimaschutzes, die Konflikte in Syrien, die Situation in Afghanistan und den Atomstreit mit dem Iran. (zu dapd-Text) Foto: Michael Gottschalk/dapd
Hollande Obama Merkel Camp David G8 Gipfel treffenHoto: dapd

Tattaunawar dai wadda aka yi ta kafar sadarwar Videoconference ta biyo bayan wadda shugabannin su ka yi yayin taron ƙasashen nan takwas masu ƙarfin arziƙin masana'antu na G8 wanda aka yi a Amurka a tsakiyar wannan watan da mu ke ciki.

Kazalika shugabannin sun zanta dangane da halin da ake ciki a ƙasar Siriya da ma dai tunanin da su ke da shi na kawo ƙarshen tashin-tashina da zub da jinin da ya ke cigaba da aukuwa tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar ta Siriya da kuma masu rajin kawo sauyi.

Shugabannin har wa yau sun jaddada buƙatar da ke akwai na samun sauyi a ƙasar ta Siriya da nufin fidda ita daga halin da ta tsinci kanta a ciki domin kare rayukan fararen hula daga salwanta da kuma jikkata da su ke yi a kulli yaumin.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammad Nasiru Awal