1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Die Lage der Nation

February 13, 2013

A cikin jawabin da ya yi ga majalisar dokokin Amirka Shugaba Barack Obama ya tabo batuttuwa da dama kama daga matsalar tattalin arziki da kuma manuoifin kasar akan kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/17dMC
Obama Rede am 12.02.2013Hoto: AFP/Getty Images

"Mun taru nan wurin ne da sanin cewa akwai milyoyin Amirkawa wadanda har yanzu ba su samu ladar aiki tukuru da kuma sadaukar da kai suka yi ba. Kara guraben aiki na zaman ginshikin tattalin arziki, to amma duk da haka akwai mutane da dama da har yanzu ke rashin aikin takaimamme."

Matsalar tattalin arzikin Amirka

Wadannan kalamai na shugaba Obama na bayyanar da irin halin ni 'yasu da tattalin arzki da ma alumar kasar baki daya ke tsintar kansu a ciki. Akan haka ne ya mika bukatar kara karamin albashi da kashi 20 daga cikin dari da kuma hada karfi da karfe a wuri daya domin ta da komadar tattalin arziki.

"Yanzu da yawan daga cikinmu mun daidata kan bukatar shigar da shirin rage gibin kudin da kasarmu ke fuskanta a matsayin bangare na ajandarmu. To amma gaskiyar itace rage gibin kudi kadai ba shi a matsayin gundarin shiri na tatalin arziki."

Obama ya kuma ba da shawarar kebe dala miliyan dubu 50 domin inganta ababan more rayuwa musamman a fannin gina hanyoyin da gadoji. Shugaban na Amirka ya mika bukatar samu dadeton raayi tsakananin bangarorin majalisar dokokin kasar guda biyu.

Manufofin Amirka akan ketare

Obama ya kuma yi magana game da manufofin kasarsa akan kasashen ketare inda yace akwai bukatar karfafa garkuwar da kasar ke da ita dubi da gwajin makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ke gudanarwa.

Overall view as U.S. President Barack Obama (R) delivers his State of the Union speech on Capitol Hill in Washington, February 12, 2013. REUTERS/Jason Reed / Eingestellt von wa
Hoto: Reuters

"Amirka za ta ci gaba da yin jagora a kokarin hana yaduwar muggan mukamai a duniya. Ya zamo wajibi gwamnatin Koriya ta Arewa ta gane cewa yin aiki da dokokin kasa da kasa ita ce kadai hanyar da za ta bi domin samar da tsaro da kuma ci gaban kanta. Takalar da ta yi a jiya ba zata haifar mata da komai ba in banda kara sanya ta zama saniyar ware. Za mu yi aiki da kawayenmu za mu karfafa garkuwarmu za mu kuma yi wa duniya jagora wajen mai martani kwakkwara game da wannan barazana"

Shugaban na Amirka ya kuma sanar da shirin kasarsa na janye fiye da rabin dakarunta da ta girke a Afganistan da yawansu yayi dubu 34 kafin farkon shekarar 2014 .

Tinkarar matsalar dimamar yanayi

Obama ya kuma yi kira ga bangarorin majalisar dokokin kasar guda biyu da su aiki tare wajen yaki da sauyin yanayi . Yace yan majalisar na bukatar samar da mafita ta bai daya da zata rage matsayin fid da hayakin dake gurbata sararin samaniya domin kare zuriyar da za a samu nan gaba.

"Domin 'ya'yanmu da kuma inganta makomar rayuwarmu muna bukatar kara himmatuwa wajen yaki da dimamar yanayi. Ko da yake gaskiya ne cewa babu wani abu daya da za mai da hankali akai, to amma gaskiyar ita ce an fuskanci shekaru 12 mafi zafi a ciki shekaru 15 da suka gabata.

Obama ya bayyana muhimmacin yin gyara ga dokokin shige da fice domin kawo sauki ga masu shaawar zuwa Amirka musamman kwararru wadanda za su taimaka wajen kirkirar da karin guraben aiki da farfado da tattalin arzikin kasar.

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani