Obama zai gana da 'yan majalisar dokoki
October 2, 2013Nan gaba kadan ne shugaban Amurka Barack Obama zai yi wata ganawa da kakakin majalisar wakilai John Boehner da Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Harry Reid gami da Nancy Pelocy da kuma Mitch McConnell da ke zaman shugabannin marasa rinjaye a majalisar wakilai da ta dattawa.
Yayin wannan gawana dai wadda za a soma ta da misalin karfe tara da rabi agogon GMT, ana sa ran Obama zai yi kokarin lallabar 'yan majalisar da su sassauto daga matsayin da suka dauka kan kasafin kudi wanda ya sanya dakatar da aiyyukan hukumomi da ma'aikatun gwamnatin kasar saboda rashin kudin tafiyar da su.
Kazalika rahotanni daga fadar mulki ta White House na cewar shugaban na Amurka zai yi amfani da taron wajen jan hankalin 'yan majalisar da su amince da wani kuduri da zai kara mizanin bashin da gwamnati za ta ci don kauracewa gaza samun kudaden tafiyar da gwamnati.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe