1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Odinga na kan gaba da yawan ƙuri´u a zaɓen Kenya

December 29, 2007
https://p.dw.com/p/Chie
Bayan an kammala ƙidayar kusan rabin yawan ƙuri´un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasar Kenya, mai ƙalubalantar shugaban ƙasa Raila Odinga ke kan gaba. Hukumar zaɓe a birnin Nairobi ta sanar da cewa Odinga ya samu ƙuri´u kimanin miliyan 2.7 yayin da shugaba mai ci Mwai Kibaki ya samu miliyan 2.1. Hasashen da tashoshin telebijin a kasar suka yi na nuni da cewa Odinga na kan gaba da yawan kuri´u. Mutane miliyan 14 suka cancanci kaɗa ƙuri´a a zabukan na shugaban ƙasa da na ´yan majalisu kafofin, to amma rahotannin sun nunar da cewa mutane kimanin miliyan takwas zuwa goma suka kaɗa ƙuri´a a zaɓukan na ranar alhamis.