1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

OPEC: Babu kari kan abin da muke fitarwa

Yusuf Bala Nayaya
May 25, 2017

Kasashen da ke fitar da albarkatun man fetir karkashin kungiyar OPEC sun shirya ci gaba da zama kan adadi na abin da su ke fitarwa na albarkatun man fetir yanzu haka.

https://p.dw.com/p/2dZRj
Algerien Opec Öl Förderung
Hoto: Reuters/R. Boudina

Ministocin da ke wannan kungiya suka bayyana haka bayan zaman da suka yi a birnin Vienna a wannan rana ta Alhamis inda suka ce za su zauna kan adadi da suke..

Kasashe mambobin wannan kungiya da wasu kasashe 11 da ke fitar da man na fetir karkashin jagorancin Rasha na fitar da man fetir da rage ganga miliyan daya da dubu 800 a kowace rana tun daga watan Janairu a kokari na samar da  yanayi da farashin na mai zai inganta.

A cewar ministan mai na Iraki Jabbar Ali Hussein al-Luiebi, wannan mataki na sake daukar watanni tara a kan abin da suke fitarwa na gangar mai a kowace rana zai taimaka masu wajen samun daidaito a kasuwa.