1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ostareliya: 'Yan jihadi zasu dandana kudarsu

Yusuf BalaMay 19, 2015

A ranar Talatan nan mahukuntan kasar Ostareliya sun bayyana matakin ba sani ba sabo ga duk wasu masu ikirarin Jihadi da ke son komawa gida koda kuwa sun sauya ra'ayi.

https://p.dw.com/p/1FRkq
Australien Premierminister Tony Abbott 2014
Hoto: Daniel Munoz/Getty Images

Wasu rahotanni dai sun nunar da cewa akwai wasu da ake zargin sun je kasashen Iraki da Siriya inda suka shiga kungiyar IS amma yanzu suke wata ganawar sirri kan yadda zasu koma gida.

A cewar wata jaridar kasar ta Ostareliya wasu mutane uku ta hanyar mai shiga tsakani, na tuntubar mahukuntan birnin Canberra koma wasu daga cikin iyalansu, kan hanyoyin da zasu bi su koma gidan, sai dai suna cike da tsoron mai zai je ya dawo ta hanyar fuskantar hukunci.

Gwamnatin wannan kasa dai ta Ostareliya mai ra'ayin 'yan mazan jiya, ta ja layi kan daukar hukunci mai tsauri ga 'yan kasar da ke shiga kungoyoyin masu jihadi bayan da aka sami rahotanni da ke nuna cewa, da dama 'yan kasar sun fita zuwa Iraki da Siriya dan bada tasu gudun mawa a yakin na masu jihadi.

A karshen shekarar bara ne dai mahukuntan na Ostareliya suka bayyana cewa duk wanda aka kama da laifin zuwa wadannan kasashe dan yaki zai iya fiskantar dauri a gidan jaru tsawon shekaru goma.

A cewar Firaminista Tonny Abbot duk wanda aka kama da laifin zuwa ayyukan jihadi doka za ta yi aiki a kansa koda kuwa ya sauya ra'ayi.