1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta janye daga yaki a Yemen

Muntaqa AhiwaApril 10, 2015

Majalisar kasar Pakistan ta amince cewar gwamnatin kasar ta tsame hannunta daga yakin hadin gwiwa da kasar Saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/1F6Ac
Pakistan Islamabad Parlament erste Sitzung Juni 2013
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Wannan mataki na majalisar Pakistan din dai ba zai rage karfin Saudiyyar a wannan yaki ba, yana dai iya zama wani abin kunya a gare ta, a kokarin da take yi na hada kan kasashe don yakar 'yan tawayen, da ake zarginsu da samun taimako daga kasar Iran.

Matakin na zuwa ne yayin da Majalisar Dinkin Duniya tare da kungiyar nan ta Red Cross suka shigar da kayan agaji a kudancin Yemen din a yau Juma'a, karo na farko tun bayan rincabewar al'amura a kasar, lamarin da ya sanya MDD bukatar samun tazara duk yini saboda mika kayayyakin na agaji.

Jami'an kasar ta Pakistan sun tabbatar da tayin aike da dakaru da Saudiyya ta yiwa Pakistan din, don murkushe 'yan tawayen na Houthi da ke fada da gwamnatin shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi na kasar ta Yemen.