1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma Francis ya gana da matasa a Filipins

January 18, 2015

Paparoma Francis ya yi kira a ziyarar da yake a Filipins da a tausayawa matasa masu yawo a titi, wadanda ke fama da matsaloli na karuwanci da kuma shan kwayoyi.

https://p.dw.com/p/1EMIY
Hoto: T.Marcelo/AFP/GettyImages

Bayan haka kuma Paparoman zai gana da matasa a kalla dubu 30, kafin wani zama na musamman na addu'a da zai jagoranta da yamma.

Daya daga cikin matasan mai suna Jun Chura dan shekaru 14 da haihuwa wanda wata kungiya mai fafutukar kariyar yara matasa ta Fondation ANAK-Tnk ta kubuto shi daga mugunyar rayuwar da ya samu kan shi a ciki, ya kwatanta halin rayuwar yara kanana wadanda iyayensu suka yi watsi da su ke ciki a wannan kasa, wadanda akasarin su ma suke fadawa tarkon masu lalata da kananan yara, yayin da wata yar yarinya yar shekaru 12 cikin kuka ta ke tambayar Paparoma cewa, wai don minene mutane kalilan ne ke taimakawa yara kanana.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba