1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya jagoranci bikin matasa

July 28, 2013

Paparoma ya nemi matasa su zage damtse wajen kawo ci-gaba tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/19FXs
Hoto: Gabriel Bouys/AFP/Getty Images

A wannan Lahadi shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Paparoma Francis, ya jagoranci rufe bikin matasa na duniya da ya gudana a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.

Paparoma ya bukaci matasan mabiya darikar kan kawar da tsoro wajen bautar ubangiji, yayin jawabi wa matasan kimanin milyan uku da suka halarci bikin, inda suka mamaye fili mai tsawon kilo-mita hudu.

Doki da murna dubban matasa suka nuna a birnin Rio de janairo na Brazil lokacin da Paparoma Francis ya hallara a bakin tekun Copacabana domin yi musu jawabi. A kiyasta cewa masu jin jini jaka kusan miliyon uku da suka fito daga kasashe 170 na duniya ne, suka halarci bukuwa na 28 na matasa da shugaban darikar Roman-katolika ya shugabanta. Baya ga Shugaba Dilma Roussef mai masukin baki, takwarorinta na Bilivia Evo Morales, da kuma Cristina Kirchner na Argentina da ke zama kasar asali ta Paparoman Francis ba a barsu a baya ba, wajen shaidar da bukukuwan na 2013.

Paparoma Francis ya ce bikin na gaba za a gudanar a birnin Krakow na kasar Poland, cikin shekara ta 2016.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe