1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ruwanda: Za a soma shari'ar shahararren dan adawa

Ramatu Garba Baba
September 14, 2020

Kotu ta caji Mista Paul Rusesabagina da laifuka na ta'addanci da samar da kungiyoyi na masu gwagwarmaya da makamai da kuma hannu a kisan jama'a a lokacin rikicin kabilancin da yayi sanadiyar rayuka kusan miliyan daya.

https://p.dw.com/p/3iT2g
Ruanda | Paul Rusesabagina | Anklage erhoben
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wata kotu a kasar Ruwanda ta caji Paul Ruse-saba-gina da laifuka na ta'addanci da hannu a kisan jama'a da kuma samar da kungiyoyi na masu gwagwarmaya da makamai.

 Dan shekaru sittin da shidan ya musanta duk laifukan a yayin da masu shigar da kara suke tuhumarsa a wannan Litinin. Wasu 'yan Ruwanda dai na ganinsa a matsayin jarumi wanda ya ceci rayukan dubban mutane ta hanyar ba su mafaka a wani otal da shi ne darakta a yayin rikicin kisan kiyashi.

Gwamnatin Ruwanda ta jima tana nemansa ruwa a jallo, amma kariya da yake samu a kasar Beljiyam ta sa aka kasa kama shi. Sai dai kuma sammacin kasa da kasa ya sa ta samu hadin kan wasu kasashen duniya wajen cafke shi. Ita dai gwamnatin Ruwanda ta zargi Ruse-sabagina da taka rawa wajen neman hambarar da Shugaba Paul Kagame da kuma kafa kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin tafkunan Afirka.