1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP na kawancen kawar da Buhari

July 10, 2018

A cigaba da kokarin neman hanyar karbe goruba a hannun kuturu, jam’iyyun adawar Najeriya sun kulla kawance CUPP da nufin kai karshen mulki na shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/319CO
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Sun dai hadu a cikin babban burin tabbatar da kai karshe na masu tsintsiya a cikin mulkin Najeriya, ga jam'iyyun adawar tarrayar  kasar kusan 40 da suka taru a Abuja suka kuma ce sun kulla kawance da nufin neman kai karshen mulkin APC a matakai daban-daban cikin kasar.

Shugaba Buhari dai ya kasa a fada ta kawancen da ya kunshi 'ya'yan jam'iyyar PDP da ma ita kanta bangare na RAPC ta Buhari da ma ragowa na kananan jam'iyyu irin nasu SDP da Labour da ragowa na da daman gaske.

Wahlkampf in Nigeria 2015
Jam'iyyun adawar dai na da buri na yi wa APC taron dangiHoto: Reuters/A. Sotunde

Akalla 'yan takara 12 na kujera ta shugaban kasar ne dai ke fata na gamewa da nufin cika burin kwace goruba a hannun kuturun, kuma  afadarsu lokaci ake jira a cewar Kabiru Tanimu Turaki da ke zaman daya a cikin masu tunanin gado na Buhari.

Kokari na rusa tattali na arziki ko kuma karatu na siyasar son rai dai, kawancen jam'iyyun na zaman sabo na salo ga masu siyasar Tarrayar Najeriya a kokarin cika buri. To sai dai kuma ya banbanta da tsari na hadakar da ya kai ga haihuwa ta jam'iyyar APC a shekara ta 2013.

Karikatur: Nigeria APC Streit
Tsakanin mambobin na APC dai an gaza samun fahimtaHoto: DW / Abdulkareem Baba Aminu

Kuma a fadar Isa Tafida Mafindi 'ya'yan jam'iyyar APC ba fargaba balle faduwar gaba ga kawancen da ya ce ba shi da tasiri ga makoma ta shugaban kasar.

Babban kalubale da ke gaban masu adawar dai na zaman hadiye buri a kokari na biya na bukata a matakai daban-daban na siyasa. Ko a jihar Kogi dai alal misali ana tafka rikici a tsakanin Jam'iyyar PDP da kuma Dino Melaye da ke zaman dan RAPC da kuma ke kokari na kulla kawancen. Abun jira a gani dai na zaman tasiri na kawancen a kokari na da ke zaman irinsa na biyu a cikin tsawon shekaru 20 na sake dawowar mulki a kasar.