1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pilipin ta yaba wa Amirka kan 'yan ta'adda

Yusuf Bala Nayaya
February 28, 2018

Sashin tsaro na Amirka ya bayyana kungiyoyin Maute da Dawlatul Islamiyah Waliyatul Masrik cikin jerin kungiyoyi na 'yan ta'adda a duniya.

https://p.dw.com/p/2tSOR
Philipinen Präsident Rodrigo Duterte
Shugaban kasar Pilipin Rodrigo Duterte dai na fama da masu tada kayar bayaHoto: Picture-Alliance/AP Photo/Bullit Marquez

Kasar Pilipin a wannan rana ta Laraba ta yaba da matakin da mahukuntan birnin Washington na Amirka suka dauka wajen ayyana kungiyoyi masu ikirarin Jihadi biyu cikin jerin sunayen ‘yan ta'adda, cikinsu kuwa har da wacce ta mamaye yankin kudancin birnin Marawi a karshen shekara bara. Mayakan da aka dauki lokaci ana ba ta kashi da su tsawon watanni biyu.

Sashin tsaro na Amirka ya bayyana kungiyoyin na Maute da Dawlatul Islamiyah Waliyatul Masrik cikin jerin kungiyoyi na 'yan ta'adda a duniya.

A ranar Talata ce dai Amirkar ta bayyana cewa za ta hana wadanda ke taimaka wa ‘yan ta'addar taba kadadrorinsu a Amirka da ma hana Amirkawa hulda da su.