1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pretoria: An tiso keyar 'yan Najeriya

March 1, 2017

Alamun kara ta'azzarar rikicin da ke a tsakanin kasashen Najeriya da kasar Afirka ta Kudu, akalla 'ya'yan tarrayar Najeriya 97 ne dai kasar ta Afirka ta Kudu ta sallamo zuwa gida.

https://p.dw.com/p/2YTvW
Matasa a Afirka ta Kudu na zargin baki da zama sila ta rasa aiki a garesu
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

An dai share tsawon makon jiya ana jeri na zanga-zanga a Abuja da nufin nunin bacin rai na jerin hare-hare ga kadarori da lafiya ta 'yan kasar da ke birane daban-daban na kasar ta Afirka ta Kudu.

To sai dai kuma daga dukkan alamu ya gaza kaiwa ga sauyin matsayi kama daga birnin Pretoria, inda mahukunta na kasar suka kauda ido tare da koro wasu jeri na 'yan kasar kusan dari a wannan mako.

Tun kafin nan dai dama sai da ta kai ga Abuja sammaci ga jakadan kasar ta Afirka ta Kudu da ke a Abuja da nufin nunin bacin rai ga hare-haren da ke zaman na kyamar baki da kuma ke neman mai da hannun agogo zuwa baya a dangantaka tsakani na bangarorin guda biyu.

To sai dai kuma duk da rai ya baci daga dukkan alamu mahukuntan na Abuja na neman kaucewa bayanai a bisa matsalar da ke neman shafar harkoki na kasuwa tsakanin juna.

Südafrika Pretoria Unruhen wegen Migranten
Daukar makami a farwa baki dai ba bakon abu ne ba a PretoriaHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Hajiya Khadija Bukar Ibrahim dai na zaman karamar ministar harkoki na wajen da aka nemi jin ta bakinta ga dawowar 'yan kasar amma kuma ta ce ba hali.

To sai dai kuma ya zuwa yammacin Laraban nan ne aka tsara wata ganawa ta musamman a tsakanin shugaban kasar Najeriyar da ke riko Farfesa Yemi Osinbajo da kuma jami'an na ma'aikatar harkoki na wajen Tarrayar Najeriya da nufin sanin girman rikicin da ma irin martanin da ya dace.

Rahotannin ta kafafe na zumunta dai sun ce an hallaka 'yan kasar sama da dari a cikin hare-haren da ke zaman na baya bayan nan da kuma Abujar ke kallon da biyu.

Moses Opkogode dai na zaman wani mazauni na Abujar da ke kallon hallaya ta matasan na Afirka ta Kudu a matsayin alamar nuna rashi na godiyar Allahu ga Najeriyar da tai uwa makarbiya wajen kwato 'yancin na bakake.

Ko a shekarar da ta shude dai da kyar da gumin goshi kamfanin na Afirka ta Kudu na MTN ya samo kansa bayan wata tarar Dalar Amirka miliyan dubu biyar din da ta nemi durkusar da harkokinsa.