1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya kalubalanci kasashen yamma

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 15, 2014

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya soki takunkumin karya tattalin arziki da kasashen yamma suka sanya wa kasarsa a kan rikicin Ukraine, inda ya ce baya bisa doka.

https://p.dw.com/p/1Dnz9
Hoto: Reuters

Putin ya bayyana hakan ne a birnin Brisbane na kasar Ostareliya gabanin taron kasashen duniya masu karfin tattalin arziki na G20. Putin ya ce takunkumin da aka sanya wa kasarsa ya saba da ka'idoji da ma burin kungiyar kasashen ta G20, har ma da dokokin kasa da kasa, kasancewar duk wani takunkumi ana sanya shi ne bisa yarjewar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Bayanin na sa na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake tsammanin minstocin kasashen nahiyar Turai za su tattauna batun yiwuwar kara kakaba wa Rashan takunkumi a kan rikicin Ukraine. Ana dai sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta gana da Shugaba Putin a kan batun rikicin na Ukraine a gefen taron kasashen na G20. A hannu guda kuma shugaban Amirka Barack Obama ya kalubalanci kasashen nahiyar Turai da su yi aiki tukuru wajen samar da ayyukan yi domin bunkasa tattalin arziki, inda ya ce Amirka ba za ta dauki nauyin karfin tattalin arzikin duniya a wuyanta ita kadai ba. Obama ya bayyana hakan ne yayin jawabin da yayi a gefen taron kasashen na G20 da suka fi karfin tatalin arziki a duniya.