1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Qatar ta soki lamirin Masar

Ahmed SalisuJune 19, 2016

Qatar ta ce daurin da aka yi wa Morsi da hukucin kisa da aka yankewa wasu mutane shidda ya saba ka'ida kuma ba a yi adalci ba wajen yanke hukunci ba.

https://p.dw.com/p/1J9Xu
Berlin Pressekonferenz Merkel al-Sisi
Hoto: picture-alliance/dpa/von Jutrczenka

Hukumomi a Daular Qatar sun yi Allah wadai da hukuncin kisan da wata kotu ta yankewa wasu mutane 6 ciki kuwa har da ma'aikatan gidan talabijin na Al-Jazeera bayan da aka zargesu da mika wa Qatar wasu takardun sirri da ke da nasaba da tsaro lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi.

A wata sanarwa da ta fidda, Daular ta Qatar ta ce hukuncin kotun na kushe da bayanai wanda ba su da tushe balle makama kuma ko kusa ba a yi adalci ba wajen yanke hukuncin. A wani martani da ta maida, ma'aikatar harkokin wajen Masar ta yi watsi da wadannan kalamai inda ta ce Qatar na kokari ne wajen goya baya ga kafafen watsa labarai da ba abin da suka sanya a gaba illa yin fito na fito da kasashe.