1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayin 'yan Najeriya kan aiyukan EFCC

Al Amin Suleiman MohammedJuly 10, 2015

Shin da wace manufa hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, wato EFCC take fadada aiyukanta a yanzu, musamman ganin cewar tsoffin gwamnoni ne suka fi shiga hannu?

https://p.dw.com/p/1FwWs
Nigeria Präsident Amtseinführung von Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Yan Najeriya na yin nazari, tare da tabka muhawa kan yaki da cin hanci da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi a wannan lokaci, inda hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta bude shafin kame tsaffin gwamnoni da ma'aikatan gwamnati da ake zargi da wawashe dukiyoyin al'umma. Cin hanci da rashawa wanda yayi katutu tsakanin ‘yan Najeriya na daga cikin abubuwan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta sha alwashin maida hankali a kai domin ganin an hukunta wadanda aka samu da wawurar kudaden al'umma, tare da kwato wadannan kudade don amfanin al'umma.

A ‘yan kwanakin nan hukumar yaki da yiwa tattali arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta kara zafafa matakan na ta, inda a cikin wannan makon kawai ta gurfanar da tsaffin gwamnonin Adamawa da Imo da Jigawa, domin fuskantar sama da fadi da kudaden al'umma da ake zargin sun yi yayinda suke gwamnati. Yanzu haka dai bayanai na nuna cewa banda tsafaffin gwamnoni uku da hukumar EFCC ta damke, ta na nan kuma ta na shirin kame wasu tofaffin gwamnonin da wasu mukarraban da suka rike manyan mukami domin amsa tuhumar da ake musu satar dukiyar kasa. Na tambayi wasu ‘yan Najeriya a fahimtar su me yasa yanzu hukumar ta zafafa ayyukanta? Ga abin da suka shaida min:

Sai dai wasu na ganin ba a nan gizo ke saka ba, akwai wadanda suka wawuri dukiyoyin kasar kuma ya zuwa yanzu an kau da kai daga garesu, wadanda kamata yayi yaki da cin hanci ya shafi kowa da kowa. Malam Umar Adamu wani mai fashin baki kan harkokin yau da kullum a Najeriya na da irin wannan tunani:

Murtala Nyako
Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala NyakoHoto: DW/U. Shehu

Duk da cewa shugaba Buhari y ace zai ja layi a binciken da wawure dukiyar al'umma da aka yi a kasar akwai masu kamata yayi yanzu a yaki cin hanci ba sani bas abo kamar yadda Alh Sale Tinka Sarkin Bodor ya shaida min.

Masharhanta da masana sun hakikan ce cewa samun nasara a yaki da cin hanci a Najeriya babbar nasara ce da zata maido mutuncin Najeriya atsakanin kasashen duniya da kuma kyautatuwar al'amura a kasa baki daya.))