1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Radadin yajin aikin likitoci a asibitin Gombe

April 12, 2013

Daruruwan marasa lafiya sun fada cikin mummunan yanayi da zai iya kaisu ga rasa rayukansu a asibitin gwamnati da ke Gombe sakamakon shiga yajin aiki na mako guda da .Kungiyar likitoci da sauran jami'an jinya ta yi.

https://p.dw.com/p/18F9V
Hoto: dapd

Mako Kungiyar Ma'aikatan kula da lafiya da suka hada da likitoci da ma'aikatan jinya da Ungozuwa za ta shafe ta na yajin aiki domin bayyana damuwar kan Karin kudin haraji da ta ce an yi wa 'yayanta. A cewar Kungiyar wannan shi ne zabi da ya saura mata inda duk wani kokarin sasantawa da hukumomin da abin ya shafa ya ci tura. Ta ce idan ba a biya mata bukantunta ba akwai yiwuwar cewa ta shiga yajin aiki na sai yadda hali yayi.

DW_Delta8
Mata masu juna biyu ba sa samun damar yin awon cikiHoto: Katrin Gänsler

Marasa lafiya sun fara tagayyara a asibitoci

A ziyarar da wakilin shashen hausa na DW ya kai asibitin Gombe da ke arewacin tarayyar Najeriya, ya tarar da marassa lafiya suna kwashe na su ya nasu don barin asibitin. Wasu masu hali na komawa asibitin kudi wadanda ba su da hali kuma ke maida marassa lafiyar su gida tare da jihar hukuncin mai duka. Malam Bala Kali Gaya wani da ke jinyar dan uwan sa da wakilinmu ya tarar da shi a asibitin yana kwashe kayan sa ya bayyana rashin jin dadin a dangane da wannan yanayi da suka samu kan su a ciki.

Ra'ayoyin game da yajin aikin likitocin Gombe

Sai dai wasu masharhanta na ganin bai kamata ma'aikatan da ke kula da lafiya su shiga yajin aiki a wannan lokaci ba saboda Yanayin da kasar ke ciki baya ga kasancewa aikin na ceton rai ne. Yajin aiki na daga cikin matsalolin dake addabar harkokin kula da lafiya a Najeriya bayan karancin likitoci da tsadar magunguna da dabi'un jami'an kula da lafiya da kuma rashin kula da hakkokin likitoci da sauran jami'an kiwon lafiya daga bangaren gwamnati. Masana na ganin cewa ya zama dole hukumomin su tashi su gyara don ceto rayukan al'umma.

Bombenanschlag auf Kirchen in Nigeria
Jami'an jinya na taimakawa idan aka kai hare haren ta'addanciHoto: picture-alliance/dpa

Yanzu haka dai Gwamnatin ta shigar da kara gaban kotu inda take son a tilastawa ‘ya yan kungiyar Likitoci da sauran jani'an jinya komawa bakin aiki saboda matakin Karin kudin haraji na bisa doka.

Rahoto da Hira cikin sauti na kasa

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe