1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rafini ya nemi hadin kan 'yan jarida kan tsaro

Abdoulaye Mamane AmadouFebruary 10, 2015

Fraiministan Nijar din ya bayyana damuwa dangane da matsaloli na tsaro sakamakon tsaurara hare haren 'yan Boko Haram a yankin Diffa da ke kan iyaka da Najeriya.

https://p.dw.com/p/1EZFy
Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012
Hoto: Getty Images

Majalisar zartarwar Nijar ta gudanar da wata tattaunawa da 'yan jarida a karkashin jagorancin fraiminista Birigi Rafini a birnin Yamai. Taron wanda ya samu halartar wasu daga cikin ministocin kasar ya duba batutuwa da suka jibanci tsaron kasar musamman yankin Diffa.

Gwamnatin Nijar din ta bayyana damuwarta dangane da irin barazanar tsaro da wasu garuruwan da ke hada iyaka da Najeriya ke fuskanta sakamakon rikicin Boko Haram, da kuma yanayin rahotanni da 'yan jarida kan gabatar dangane da wasu labarai da ke da nasaba da tsaro.

Birigi Rafini ya nemi fahintar juna tsakanin tsakanin hukumomi da 'yan jarida, ta yadda za su samu bayani da suke bukata a maimakon amfani da jite-jite. Su kuwa 'yan jarida bayyana damuwa suka yi dangane da yadda basa samun tsabtataccen labari kan bayanan da suke muradin amfani da su.

Nijar din dai ta yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen yakar mayakan na Boko Haram.