1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Amnisty a game da hukuncin kissa a dunia.

April 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1J

Hukumar kare hakokin bani adama ta dunia Amnisty Internatiopnala ta hiddo rahoron ta na sheakara a shekara ageame da halinda a ke ciki a dunia ta fanninhunkunci kissa.

Wannan rahoto ya ce, a yanzu haka, a jimilice, mutane dubu 20 ne, a faɗin dunia baki ɗaya, ke cikin faduwar gaban fuskantar hukunci kissa.

Sannan a shekara da ta gabata, mutane 2.148 a ka yanke wa hukuncinkissa a dunia , kuma kashi 94 bisa 100 ysa wakana, a ƙasashe 4, da su ka haɗa da, Amurika, Iran, China, da Saudiyya.

A China, mutane 1.770 ne, a ka yankewa hukunci rajamu, 94 a Iran, 86 a Saudi Arabiya ,sannan 60 a ƙasar Amurika a shekara ta 2005.

Rahoto ya ce akwai alamun ma addadin mutane ya zarta hakan ta la´akari da yadda hukumomi ba su cika bayyana iri wannan hukunci ba.

Saidai a dan samun ci gaba a ƙasashe kamar su Amurika, inda a shekara bara, a ka soke dokar hukuncin kissa ga ƙananan yara.

A ƙarshe rahoton, yayi kira ga gwamnatoci, da ƙungiyoyin na dunia, da su haɗa ƙarfi domin yaƙar hukuncin kissa, da ya sabawa dokokin kare haƙoƙin bani adama.