1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar Cutar Kanjamau ta Duniya

December 1, 2005
https://p.dw.com/p/BvIa

A yau ake bikin ranar cutar kanjamau ta duniya,tare shirya taruruka da nufin kara wayar da kan jamaa game da illar wannan cuta da bata da magani.

Shugaban shirin yaki da cutar kanjamau na Majalisar Dinkin Duniya,yace a wannan shekarar an samu karuwar yawan wadanda suka kamu da cutar ,wadda aka kiyasta sun kai mutum miliyan 40 da dubu dari uku,wadda rabinsu mata ne.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta bukaci kasashen duniya da su kara maida hankalinsu tare da kara ware makudan kudade don yaki da cutar.