1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar kece raini tsakanin Obama da Romney

November 6, 2012

Yau ce ranar da al'umar Amurka su ka jima su na dako domin zaɓen sabon shugaban ƙasa tsakanin Shugaba Barack Obama da kuma da Mitt Romney na Republican. Kana ana gudanar da zaɓen 'yan majalisu.

https://p.dw.com/p/16dr9
Hoto: Reuters

Tun da sanyin safiya ne dai al'ummar Amurkan su ka bazama rumfunan zaɓe domin ƙaɗa ƙuri'unsu ga ɗan takara da su ke ganin zai fi dacewa ya jagorancin ƙasar. Baya ga zaɓen na shugaban ƙasa, har wa yau 'yan Amurkan na zaɓen wakilai na majalisun dokokin ƙasar biyu waɗanda za su wakilce su wajen yin dokoki a ƙasar.

A Manhattan da ɗaukacin New Jersy da Connecticut da ma sauran wuraren da mahakauciyar guguwar nan ta Sandy ta yi ta'adi ana kaɗa ƙuri'u kamar sauran jihohin ƙasar sai dai ana yin amfani ne da ƙuri'u na takarda saɓanin kwamfuta da ake amfani da ita a sauran wurare kamar yadda aka saba, hakan kuwa ya zama dole saboda rashin hasken wutar lantarki, lamarin da ya sanya mutanen yankunan ɗaukar tsawon lokaci kafin kaɗa ƙuri'unsu.

Wahlen USA 2012
Hoto: Reuters

Yayin da Amurkawa ke kaɗa ƙuri'un na su domin tantance gwaninsu, a gefe guda kuma Barack Obama na jam'iyyar Demokarat ya ziyarci jiharsa ta Chicago yayin da abokin hamayyarsa Mitt Romney na jam'iyyar Republican ya ziyarci jihohin Ohio da kuma Winsconsin domin sake lallabar masu kaɗa ƙuri'u.

Barack Obama US Wahl Ohio
Hoto: AFP/Getty Images

''Shugaba Barack Obama ya ce bayan watannin da aka share ana yaƙin neman zaɓe da ma kuɗaɗen da aka kashe, yanzu zaɓi ya rage naku. Abun baya hannuna, ya na hannunku. Komai ya danganta da abin za ku yi''.

Shi kuwa Mitt Romney wanda ya samu rakiyar mai dafa masa a wannan tafiya da su ke ta ƙalubalantar Obama a zaɓen na shugabancin Amurka a ziyarar da ya kai Ohio, cewa ya yi masu kaɗ ƙuri'a da su ka amince su zaɓe su daure su shawo kan sauran mutane domin su kaɗa masa ƙuri'a.

Ya ce ''yanzu wataƙila wasu daga cikin abokan ku da danginku ba su yanke shawarar wanda za su zaɓa ba, ina son ku tabbata kun yi musu magana don ganin ko za ku iya sanyasu su kasance tare da mu. Ku gaya musu kada su yi la'akari da jawabai da kuma tallukan da rinƙa sanyawa da dai sauransu''.

Mitt Romney und seine Frau bei der Wahl
Hoto: AFP/Getty Images

A halin da ake ciki dai dukannin jihohin hamsin na Amurka sun ɗau harami dangne da wannan zaɓen inda al'ummar Amurka musamman ma dai waɗanda shekarunsu su ka kai kaɗa ƙuri'a su ka kan layauka domin zaɓe.

Galicia Malone na daga cikin masu kaɗa ƙuri'a a Illinois, wadda kuma ke kan hanyarta ta zuwa asibiti domin haihuwa, ta ce wannan shi ne karon ta na farko na yin zaɓe. Ta kuma ce duk da ta na cikin wani yanayi sai ta kaɗa kuri'a kafin isa asibiti domin hakan zai sauya rayuwarta da ma dai abin da za ta haifa.

Ita ma Susan Holiday wadda ta bi dogon layi a New Jersy don kaɗa ƙuri'arta ta ce za ta kasance kan layi duk kuwa da cewar layin baya ja sosai domin a cewarta ba za ta bari a yi ba ita ba.

Wahlen USA 2012
Hoto: Reuters

Da misalin ƙarfe 12 GMT ne dai ake sa ran samun sakamakon farko na ƙuri'un da aka kaɗa a wasu jihohin yayin da ake sa ran samun ƙarin wani sakamakon daga sauran jihohin zuwa tsakar dare.

Har kawo wannan lokacin da na ke haɗa wannan rahoton dai, 'yan takarar biyu na yin kan-kan-kan ne kuma abu mai wuya ne a ce a wannan halin a tantance wanda zai lashe zaɓen. hausawa dai na cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.

Wahlen USA 2012
Hoto: Reuters

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani