1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar ma'aikata a cikin matsalolin rayuwa

May 1, 2014

Katsalandan siyasa, da karancin albashi, da tsadar ruyuwa, da kuma rashin cika alkawura daga hukumomi, na daga cikin matsalolin da ma'aikata ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/1Bs8j
1. Mai-Kundgebung in Abuja
Hoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Ranar daya ga watan Mayu ko wace shekara, rana ce da Majalissar Dinkin Duniya
ta kebe a matsayin ranar ma'aikata a duk fadin duniya, wadda kuma ma'aikatan ke yin amfani da wannan rana su yi nazari a kan matsalolin da kuma kalubale da suke fuskanta.

Ma'aikata musamman a kasashen Afirka suna kokawa da rashin samun albashi. Ga kuma rashin ingantattun kayan aiki sai kuma uwa uba yawan shisshigi daga 'yan siyasa.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ma'aikatan ke nuna yatsa ga 'yan siyasa a matsayin zargi ga rikitar da sashen ma'aikatan gwamnati. Mallam Sheriff Issufu magatakardan hadaddiyar kungiyar kwadago ta CNT a jamhuriyar Nijar da ta kunshi akalla kungiyoyi 44 ya ce lamarin ya fi muni a jihar Tawa.

Katsalandan siyasa a harkar ma'aikata

Abuja 1. Mai-Rallye
Hoto: DW/Uwais Abubakar Idris

A nashi bangaren, Mallam Ibro Souley magatakardan hadaddiyar kungiyar CDTN ita ma da ta hada kungiyoyin kwadago da dama, ya ce ko baya ga katsalandan na siyasa su na da jerin matsalolin na daban, abin da ke janyo yaje-yajen aiki.

To sai dai Mallam Ibrahim Miko, kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya a fuskar jihar Tawa, ya yi watsi da zargin.

Yajin aiki dai a kasashe irinsu tarayyar Najeriya da jamhuriyar Nijar ya zama ruwan dare ga ma'aikatan sanadiyar abin da ake gani tamkar wasa da hankalin masu aikin kwadagon, sha'anin da ko shakka babu ke taimakawa wajen karayar karfin tattalin arzikin kasa.

Mawallafa: Ardo Hazzad / Issofou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal