1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaƙi da cin hanci ta duniya

December 9, 2013

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware wannan rana ta masamman domin yin bita, kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a tsawon shekara wajen yaƙi da cin hanci.Nijar ta bi sahun sauran ƙasashen wajen karama wannan rana.

https://p.dw.com/p/1AVZs
Symbolbild Schmiergeld
Hoto: picture alliance/ZB

Ƙungiyoyin farar hula sun bayyana takaicinsu dangane da yadda cin hanci da handame dukinyar ƙasa suka samu gindi zama a Nijar Wanda kuma suke zargin hukumomin ƙasar da rufe ido kan wannan matsala.

Hukomin Nijar su gaza magance matsalar cin hanci wadda ta yi katutu a ƙasar

Nijar,wadda ba a san ta ba da ɗabi'ar cin hanci can baya,amma ɓula siyasa na daga cikin abin da ya kawo cin hanci da yin sama da faɗi da dukiyyar jama'a. Duk wani ɗan siyasar da ke son mulki, ya kan yi iƙirarin cewar zai kauda lamarin na cin hanci ,amma kuma da zaran ya hau kan kujerar mulkin sai ya manta. Nasiru Sa'idu,shugaban wata ƙungiyar farar hula da ke gwagwarmayar kyautata rayuwar talakawa,wato Muryar tallaka,ya nuna takaicinsa ganin yadda ake ci hanci a Nijar. Ya ce : ''Cin hanci da karɓar rashawa sosai, suna faruwa a Nijar,babu ta yadda za a cewa talaka ana yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa ya yarda domin bai ga an taɓa hukunta waɗanda ke satar kuɗaɗen ƙasar ba.'' Shugaban ƙasar Nijar ,Alhaji Mahamadou Issoufou,kafin ya hau kan kujerar mulki ya yi iƙirarin cewar zai kauda cin hanci da yin babakere da dukiyar ƙasa,amma har yanzu jama'a ba su gani ba a ƙasa. Duk kuwa da cewar ya girka wasu hukumomin da ke binciken waɗanda suka ci dukiyyar ƙasa,kamar HALCIA,da wani layin tarho na ba da damar duk wanda aka yi ma shari'a idan akwai cin hanci ya kira don ba da labari. Alhaji Idi Abdu,shi ne kakakin hukumar. Ya ce : ''Inda ka kai kuka wajen alƙali sai ka yi jira ya yi bincike ,saboda haka mu mun kai ƙara kuma muna jiran sakamako. ''

Sitzung des Parlaments in Niger
Yan majalisar dokokin Nijar masu tsara dokokiHoto: DW/M. Kanta

Cin hanci na zubar da martaba da darajar ƙasa

Cin hanci dai ko karɓar rashawa,da handame dukiyyar ƙasa,bayan maida tattalin arzika baya,yana zubar da mutumcin ƙasa a idon duniya. Babban abin da magabata yakamata su yi shi ne su yi adalci da fidda son rai a zukatansu domin magance wannan matsala a cewar Nasiru Sa'idu ,Muryar talaka. Ya ce :'' Kamar yadda shugaban ƙasa ya ce yana yi don talakawa,kuma shi ne Allah ya ɗora wa nauyin jama'a ya tabbatar da ganin a hukunta duk wani wanda aka samu da laifin yin sama da dukiyyar ƙasa, ta haka kwai za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa.'' A albarkacin wannan ranar shugabannin ƙungiyoyin fara hula sun shirya shagulgulan na faɗikar da jama'a, a kan maganar ta yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa a duk faɗin ƙasa.

Symbolbild Geldgeschenk
Hoto: picture-alliance/dpa

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Lagas Mansur Bala Belo ya aiko mana a kan wannan ranar ta yaƙi da cin hanci dangane da yadda lamarin yake a Najeriya.

Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani