1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsar da sabuwar gwamnatin Italiya

April 28, 2013

Wata 'yar asalin Kongo ta sami wakilci a sabuwar majalisar ministocin Italiya.

https://p.dw.com/p/18ObO
Italy's Integration minister Cecile Kyenge (L) stands during the swearing in ceremony in Rome of the new government of Prime Minister Enrico Letta on April 28, 2013. Italy's new coalition government was sworn in on Sunday, bringing fresh hope to a country mired in recession after two months of bitter post-election deadlock watched closely by European partners. AFP PHOTO / VINCENZO PINTO (Photo credit should read VINCENZO PINTO/AFP/Getty Images)
Hoto: VINCENZO PINTO/AFP/Getty Images

Wani dan bindiga ya yi ta harba harsasai a kusa da fadar gwamnatin Italiya, daidai da fara bikin rantsuwar sabuwar Majalisar Ministoci da aka girka jiya bisa jagorancin Firaminista Enrico Letta.

Jami'an tsaro sun cafke wannan mutum, kuma sun fara bincike domin gano mussabbabin kai harin. Dan sanda daya dai ya samu rauni, da kuma shi dan bindigar.

Sabuwar gwamnatin ta gamin gambiza, ta kunshi membobin jam'iyyar gurguzu da ta jari hujja masu adawa da juna, da kuma masu sassaucin ra'ayi.

Sai dai bangarorin sun samu mahada guda, a kan batutuwa biyu masu mahimmanci, hasali ma kubuto Italiya daga matsanancin halin da ta shiga, sannan dukkansu suna adawa da matakan tsimi da tanadi, da kungiyar Tarayya Turai ta tilastawa kasashe membobinta.

A lokacin bikin rantsuwar shugaban kasar Italiya Georgio Napolitano, ya yi kira ga gwamnatin ta ba marada kunya.

Wannan gwamnati, ta kunshi mata da matasa da dama, abinda ba a saba gani ba, a tsarin siyasar Italiya. Kazalika a karon farko an nada wata bakar fata 'yar asalin Kongo a matsayin minista. Bayan bikin rantsuwar a wannan Litinin(20.04.2013) Firaminista Letta zai gabatar da jawabi gaban Majalisar Dokoki, domin fayyace tsarin aiki da zai gudanar.

Mawallafi : Yahouza Sadissou
Edita : Saleh Umar Saleh