1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsar da shugaba Bush na Amurka

January 21, 2005

A cikin jawabinsa na amincewa da mubaya#ar da aka yi masa shugaba George W. Bush na Amurka ya lashi takobin shigar da abin da ya kira 'yanci da walwala a dukkan sassan duniya

https://p.dw.com/p/BvdY
Bikin rantsar da shugaba Bush
Bikin rantsar da shugaba BushHoto: AP

A karkashin tsauraran matakai na tsaro aka yi bikin rantsar da shugaba George Bush na Amurka domin wani sabon wa’adin mulki karo na biyu. A cikin jawabinsa na amincewa da mubaya’ar da aka yi masa, shugaban na Amurka yayi wasu tsauraran alkawurruka masu firgitarwa. Domin kuwa shugaba Bush yayi alkawarin yin amfani da karfi da kuma angizon da Amurka ke da shi wajen shigar da abin da ya kira wai ‚yanci da walwala a dukkan sassa na duniya. Duk masu mulkin fir’aunanci, a ko’ina suke a duniya, ba su da sauran kwanciyar hankali, in ji shi. Sannan ya ce su kansu Amurkawan ba zasu ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba, sai fa idan sun taimaka aka shigar da demokradiyya a dukkan sassa na duniya. Wadannan kalaman dai tamkar ba a ce a kunnuwan ainifin mutanen dake fama da mulkin danniya da kama karya a duniyar nan tamu. Domin kuwa ana ci gaba da take hakkin ‚yan Adam kama daga Masar zuwa China ko Pakistan zuwa Uzbekistan. Amma fa kawo yanzun shugaba Bush bai fito fili ya ce uffan game da haka ba. A hakikanin gaskiya ma dai kasar Amurka tana ci gaba da ma’amalla ta kut-da-kut ne da ‚yan mulkin danniya da kama karya dake biyayya ga maslaharta. Maganar samar da ‚yanci da walwalar ta shafi wata manufa ce ta yada angzon Amurka kama daga yankin Hindukush ya zuwa mashigin tekun pasha. Misali kasar Iraki a yanzun ta zama tamkar zakaran gwajin dafi ne dangane da ikon da Amurka ke da shi na maye gurbin wani mulki na kama-karya da wani tsarin mulki na demokradiyya a zaben kasar da za a gudanar nan gaba a wannan wata. Idan har an samu wata ‚yar nasara ta samar da kwanciyar hankali a karkashin wani tsari na demokradiyya a kasar ta Iraki, to kuwa ba shakka sauran ‚yan mulkin kama-karya zasu shiga hali na zaman dardar. Amma idan har murna ta koma ciki dangane da katsalandan sojan Amurka aka kuma ci gaba da zub da jini a kasar Iraki to kuwa shugaba Bush zai rika shan tofin Allah tsine a duk lokacin da aka ambaci sunansa a kundin tarihi. Bugu da kari kuma shugaban zai dada fuskantar matsin lamba a cikin gida domin janye sojojin Amurka daga harabar Iraki. Abu mafi alheri ga kasar Amurka shi ne ta ba da fifiko ga manufofi na diplomasiyya a kokarinta na yada mulkin demokradiyya a maimakon neman yin amfani da kan bindiga. Ta haka ne kawai zata iya samun goyan baya daga su kansu ainifin mutanen da lamarin ya shafa, kamar dai yadda aka gani dangane da gagarumin taimakon da ta bayar ga yankunan da bala’in tsunami ya rutsa da su. Makomar alkawururrukan da George Bush ya lashi takobi akansu dai ta danganta ne da irin ci gaban da za a samu a Irak da Yankin Gabas ta Tsakiya da kuma shawarwarin da ake yi da Iran a game da shirinta na makamashin nukiliya. A nan ya kamata Bush ya nuna cewar lalle ya cancanci jan akalar siyasar duniya ta yadda za a wayi gari ana haba-haba da kasar Amurka a matsayin mai yada mulkin demokradiyya zuwa sauran sassa na duniyar. Amma a halin da muke ciki yanzu akwai tababa game da haka.