1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rarrabuwar kawuna a kan aikin soji a Krimiya

March 6, 2014

Kungiyar Tsaro da hadin kan kasashen Turai ta amsa kirar da gwamnatin Ukraine ta yi mata na turawa da sojoji domin tabbatar da zaman lafiya a wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1BLHR
Krim Soldaten Belbek 06.03.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Sojoji 35 da ba su dauke da makamai wadanda kuma suka fito daga kasashe 18 na Turai ne suka yi tattaki i zuwa Yukren tun a ranar laraba da ta gabata. Daga cikin Kasashen da suka bayar da gudunmawar sojoji har da tarayyar Jamus da Faransa da Birtaniya da Amirka da kuma Poland. Wadanda sojojin na kungiya tsaro da hadin kan Turai za su fara ya da zango ne a birnin Odessa da ke kudancin Yukren, kafin daga bisani su isa tsibirin Krimiya da ake takaddama a kai tsakanin Rasha da kasashen yammavcin dunyia. Turawa da ayarin sojoji karkashin kungiyar OSCE ba wani sabon abu ba ne a nahiyar Turai. So 90 ne dai kungiyar tsaro da hadin kai ta Turai ta tura da irin wannan tawaga a ckin shekaru 15 da suka gabata. Ko da ita ma Yukren ta yi amfani da yarjejniyar birnin Vienna wajen neman taimakon wannan kungiya. Wolfang Richter wanda kwararren ne a fannin tsaro ya bayyana irin nauyin day a rataya a kan dakarun na OSCE a Yukren

"Za su je wuraren da wutar rikicin ke ci gaba da ruruwa ciki kuwa har da tsibirin krimeya domin gane wa idanunsu a bin da ke faruwa a can. sai dai idan suka isa Kremiya, za mu gani ko za su samu damar shiga koko a 'a. Yukren ta gayyaci wadannan sojojin na OSCE ne a matsayin ta na 'yantaciyar kasa. Sai dai inda gizo ke sake shi ne yadda za ta kaya da wadanda ke ikirarin kare yankin, ma'ana ko za su kyale sojojin da ke sa ido su gudanar da aikinsu."

Babban nauyin da ke gaba tawagar sojojin na Turai da ke sa ido dai, shi ne gudanar da bincike domin sanin yawan makamai da ke a kasar ta Yukren da kuma yawan sojojin da suka ja daga. kana za su bayar da shawarwari ga shugabannin Turai a cikin rahoton da za su mikasu game da hanyoyin da ya kamata a bi dominshawo kan rikicin a yukren a fannin tsaro.

EU Krisengipfel zu Ukraine 06.03.2014 Brüssel Merkel Jazenjuk
Hoto: Reuters

Tuni dai kasar Rasha ta nuna shakkunta a kan rawar da sojojin na OSCE za su iya takawa wajn warwaren rikicin na Yukren. Fadar mulki ta Moscow ta nunar da cewa makamancin wannan tawaga da kungiyar tsaro da hadin kan turai da aka tura a Osetiya ta kudu ba a bin da ta tsinana illa dada dagula al'amura a wannan kasa

Amma kuma Wolfgand Richter ya nunar rundunar ta OSCE ba ta da wani hurumin da ya fi sa ido an yadda al'auma ke gudana a kasa kamar Yukren da ke fama da rikici.

"Domin a samar da maslaha, abu ne mai muhimmanci a tura da dakarun kasa da kasa inda ake rikcii, domin su gano hakin da ake ciki domin sanar da membobin wannan hukuma domin su dauki matakin da ya dace. Tarihi ya nuna cewar turawa da dakaraun kasa da kasa na taikamawa wajen kantar da kurar rikicin."

Ita a takaice dai sojojin za su tantace ko sojojin da ke jibge a tsibirin Krimiya daga rasha suka fito ko kuma sojojin sa kai kamar yadda gwamnatin Putin ta bayyana. da dai kungiyar OSCE, ita ce ta maye gurbin CSCE da aka kirkiro a zamanin yakin cacar baka tare da taimaka kawo karshe sa in sa da ke tsakanin tarayyar Soviet da kasashen yammaci duniya.