1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun kame wani fitaccen dan jarida a Rasha

Abdourahamane Hassane
June 8, 2019

A Kasar Rasha hukumomi na tsare da fitaccen dan jaridar nan, Ivan Golounov wanda ya shahara a kan aikin jarida na binciken ko-kop.

https://p.dw.com/p/3K4Qy
Russland Journalist  Ivan Golunov
Hoto: Reuters/T. Bekbulatova

Ana dai zargin dan jaridar ne da safara hodar cocaine mai yawan gaske a cikin jakar da yake dauke da ita a baya. 'Yan sanda sun ce sun kamashi dauke da hodar ta cocaine kilo hudu. Ivan Golounov wanda ke aiki a jaridar Meduza mai zaman kanta a Rasha  ya cika sukar gwamnatin a rubuce- rubuce da yake yi.