1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Iran za su ci gaba da yin aiki tare

Ramatu Garba Baba
November 1, 2017

Shugaba Vladimir Putin ya jadadda karin goyon bayan Rasha ga Iran na marawa kasar baya a wannan lokacin da ta ke fuskantar barazana ta watsewar yarjejeniya da ta cimma kan shirin nukiliyarta.

https://p.dw.com/p/2msE9
Iran Wladimir Putin & Hassan Rohani in Teheran
Hoto: picture-alliance/dpa/TASS/M. Metze

Shugaba Hassan Rouhani a na shi bangaren ya yaba da dangantakar da ke a a tsakaninsu na bunkasar tattalin arziki da kuma yadda suke yaki da ayyukan ta'addanci a yankunansu. A yarjejeniyar da aka kulla da Iran da wasu kasashen duniya shida, Iran ta amince ta takaita shirinta na nukiliya inda a daya bangaren za a janye takunkumin da aka sanya ma ta.

Amirka karkashin mulkin shugaba Donald Trump ta yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar don a cewarta Iran ta sabawa dokokin da yarjejeniyar ta gindaya. Kasashen Britaniya da Chaina da Faransa da Jamus da Rasha da kuma kungiyar EU da suka kulla yarjejeniya sun ce za su ci gaba da aiki da ita duk da matakin Amirka na janyewa.