1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na son shiga tsakanin Indiya da Pakistan

Zulaiha Abubakar
February 28, 2019

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewar kasarsa a shirye take ta wuce gaba don sulhunta rikicin da ke tsakanin kasashen Indiya da Pakistan masu makwabtaka da juna.

https://p.dw.com/p/3EFiq
Sergei Lawrow Außenminister Russland
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Prokofyev

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da Firaministan Indiya Narendra Modi ya nemi al'ummar kasarsa su zama tsintsiya madaurinki daya a lokacin da yake wani jawabi cikin fushi, sakamakon cafke matukin jirgin kasar da Pakistan ta yi daidai lokacin da kasashen biyu masu makaman nukiliya ke nuna wa juna yatsa.

Tuni Indiya ta rufe filayen saukar jirage hudu da ke arewacin kasar bayan jiragen yakin Pakistan sun kutsa wani yankin kasar Indiya da ke Kashmir, sabon rikicin dai ya samo asali ne sakamakon musayar wutar da kasashen biyu suka yi a kan iyakar yankin Kashmir, wanda kowacce kasa ke ayyanawa a matsayin mallakinta.