1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ba wa Snowden karin wa'adin zama.

August 7, 2014

Edward Snowden da Amirka ke nema ruwa a jallo ya sami karin wa'adin zama a Rasha.

https://p.dw.com/p/1Cqyl
Edward Snowden Asyl in Russland
Hoto: picture-alliance/dpa

Mai kwarmata bayanan nan dan asalin Amirka Edward Snowden ya sake samun takardar ci gaba da zama a kasar Rasha har na tsawon shekaru 3, kamar yadda lauyan da ke kare shi ya bayyana a ranar Alhamis dinnan.

A shekarar da ta gabatane mahukuntan na birnin Moscow suka bada damar zama ga Snowden na tsawon shekara guda, wacce ta kare a ranar daya ga watannan na Agusta.

Anatoly Kucherena shine lauyan da ke kare mista Snowden:

"An dauki mataki kan takardun neman karin waadin da muka gabatar wanda daga ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2014 Snowden zai ci gaba da zama a wannan kasa har tsawon shekaru 3".

Tun bayan da ya samu takardar wucin gadi ta zama a wannan kasa baa sake jin labarin inda yakeba, wannnan mataki kuma na mahukuntan na Rasha ya sake rura wutar takun sakar da ke tsakaninsu da Amirka.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal