1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta jibge sojinta kan iyakar Ukraine

April 19, 2014

Mahukuntan Rasha sun ce sun girke sojinsu ne kan iyakar kasar da gabashin Ukraine ya Allah ko rikicin da ke faruwa a kasar zai iya tsallakowa zuwa cikin kasar ta Rasha.

https://p.dw.com/p/1Bl5o
Ostukraine Krise Kramatorsk 16.04.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Mai magana da yawun shugaban Rasha Vladmir Putin, Dmitry Peskov ya ce sojin da aka kai yanzu za su dafa wa takwarorinsu da aka rigaya aka girke tun a baya don su kare kasarsu daga dukannin wata barazana da za ta iya fuskanta.

Mr. Peskov ya ce Ukraine fa kasa ce da ya ce an yi juyin mulki don haka dole ne wadanda ke makwabta da ita su yi taka-tsantsan, kuma Rasha a matsayinta na kasar da ke cin gashin kai ta na da dukkanin 'yanci na kare kanta daga kowacce matsala da ka iya tunkaro ta.

Masu sanya idanu kan rikicin siyasar Ukraine dai na ganin wannan matakin da Rashan ta dauka zai sake tsananta irin zaman doya da man jan da kasashen biyu ke yi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe