1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta fara sayar da makamai ga Iran

Lateefa Mustapha Ja'afarApril 13, 2015

Isra'ila ta fito fili ta soki matakin da Rasha ta dauka na dagewa Iran takunkumin sayar da makamai ta hanyar shirin sayar mata da makaman kakkabo jiragen yaki.

https://p.dw.com/p/1F7Kx
Javad Zarif na Iran da Sarge Lavrov na Rasha
Javad Zarif na Iran da Sarge Lavrov na RashaHoto: Reuters

Ministan kula da al'amuran tsaron sirri na Isra'ilan Yuval Steinitz ya bayyana hakan inda ya ce wannan na nuni da cewa Iran za ta yi amfani da bunkasar tattalin arzikin da za ta samu sakamakon cimma yarjejeniya kan makamashin nukiliyar tata ta hanyar sayen makamai amma ba kyautata rayuwar al'ummarta ba. Rasha dai ta ce Iran na da damar mallakar makaman kasancewar an cimma matsaya dangane da batun makamashin nukiliyarta da aka yi ta takaddama a kai. Ita ma ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta fito fili ta bayyana rashin gamsuwarta da wannan mataki da Rashan ta dauka, sai dai ma 'aikatar cikin gidan Amirkan ta ce wannan ba zai yi nakasu ba ga kokarin cimma matsayar karshe tsakanin Iran din da kasashe shida masu karfin fada a ji a duniya kan batun makamashin nukiliyar na Iran.