1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas kan juyin mulki a Burundi

Ahmed SalisuMay 13, 2015

Sojoji a Burundi sun sanar da hambarar da shugaban kasar Pierre Nkurunziza daga gadon mulki, sai dai fadar shugaban kasar ta ce babu kanshin gaskiya a lamarin.

https://p.dw.com/p/1FPV5
Pierre Nkurunziza
Hoto: I.Sanogo/AFP/GettyImages

Sojin na Burundi karkashin ikon wani janar mai suna Godefroid Niyombare suka ce sun hambarar da gwamnatin shugaba Nkurunziza har ma ya shaidawa manema labarai cewar sun dufufa wajen ganin sun girka gwamnati ta rikon kwarya to sai dai fadar shugaban kasar ta ce wannan batu daidai ya ke da wasan yara, yayin da masu adawa da mulkin shugaban kasar a nasu bangaren suka fantsama kan tituna inda suka yi ta sowa don nuna murna.

Jim kadan bayan da fidda wannan sanarwa ta yin juyin mulki da sojin suka ce sun aiwatar, mahukuntan Tanzaniya inda shugaba Nkurunzizan ke hallartar wani taro na shugabannin kasashen gabashin Afirka suka ce shugaban na Burundi ya kama hanyarsa ta komawa gida don tinkarar kalubalen da ke gabansa.

Militärputsch in Burundi
Al'ummar kasar sun yi ta zanga-zanga ta adawa da tazarcen shugaban BurundiHoto: Reuters/G. Tomasevic

Shakku game da tabbatar juyin mulkin

Fitar wannan labari na komawa gida da aka ce shugaban na Burundi ya yi ya sanya shakku a zukatan mutane da dama kan nasara ko akasin haka na yin juyin mulki sai dai a wani abu mai kama da maida martani ga batu, Janar Niyombare da ya jagoranci juyin mulki ya sanar da rufe kan iyakokin kasa da na ruwa kana ya umarci hana sauka da tashin jirage a kasar.

Burundi Proteste gegen den Präsidenten Nkurunziza
An zargi jami'an tsaron Burundi da yin amfani da karfi kan masu zanga-zangaHoto: Getty Images/AFP/L. Nshimiye

Kiran maida Burundi kan tafarkin dimokradiyya

Tuni dai shugabannin yankin gabashin Afirka suka bayyana rashin amincewarsu da wannan juyin mulki da sojin suka yi a kasar ta Burundi. Shugaban Tansaniya da ya yi magana da yawun shugabannin ya ce wannan batu ne da ba za su lamunta ba kuma sun bukaci da maido da tsarin mulkin farar hula a kasar ba tare da bata lokaci ba.

Wannan batu na juyin mulkin dai na zuwa ne lokacin da kasar ke tsada riki na siyasa biyo bayan shirin shugaban kasar na yin tazarce, matakin da al'ummar kasar da dama suka ce ba su amince da shi ba kasancewar hakan yin karen tsaye ga kudin tsarin mulki ko da dai a 'yan kwanakin da suka gabata kotun kundin tsarin mulkin kasar ta sanar da sahale masa sake neman shugabancin kasar a karo na uku.