1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar baki a zaben Jamus

Ahmed Salisu
September 7, 2017

Yayin da zaben gama-gari na Tarayyar Jamus ke kara karatowa, wani lamari da ake ci gaba da sanya idanu kan zaben na bana shi ne irin rawar da Jamusawan da ke da tushe daga kasashen waje za su taka a wannan zabe.

https://p.dw.com/p/2jVeB
Deutschland Aydan Özoguz
Hoto: picture alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Jamus dai na zaman guda daga cikin kasashen Turai da ke da yawan mutane da suke da tushe daga kasashen waje ciki kuwa har da Turkiyya. Wannan batu ya sanya wasunsu shiga a dama da su a fagen siyasar kasar har ma kimanin 37 daga cikin irin wadannan mutane suka kasance 'yan majalisar dokokin kasar kuma suke rike da mukamai manya. Wadannan mutanen dai sun fito ne daga jam'iyyu daban-daban na kasar ciki kuwa har da manyan jam'iyyun kasar biyu wato CDU ta Shugabar gwamnati Angela Merkel da kuma jam'iyyar SPD da ke adawa.

Baya ga irin wadannan mutane, a share guda akwai dama musamman ma matasa da ke rike da fasfo din Jamus kasancewar guda daga cikin iyayensu na da tushe daga wata kasa ta daban wadda ba Jamus ba wanda suka isa kada kuri'a. Masharhanta dai na ganin irin yadda jam'iyyun da ke kyamar baki ke kara matsa kaimi na ganin sun samu wani kaso na kujerun majalisar dokokin kasar kan iya sa wasu tashi haikan wajen jan hakalin mutane na su kada kuri'unsu a zaben. Aydan Özoguz da ke da tushenta daga Turkiyya kana ta ke zaman mataimakiyar shugaban jam'iyyar SPD mai adawa na da irin wannan ra'ayi:

Deutschland Aydan Özoguz
Aydan Özoguz a tsakiya ta yi fice a siyasaHoto: picture alliance/dpa/B. von Jutrczenka

"Dole ne a kara matsa kaimi wajen wayar da kan mutane a shaida musu cewar idan ka na son kare 'yancinka ta hanyar da doka ta tanada to fa dole ne ka shiga a dama da kai a harkokin zabe da ke tafe."

Yayin da wasu 'yan siyasa ke fafutuka wajen ganin sun ja hankalin masu kada kuri'a musamman masu tushe daga waje kan su zabi jam'iyyun da za su kare muradunsu, wasu na ganin kyautuwa ma ya yi a ce majalisar dokokin kasar ta samu karin baki. Karamba Diaby da ya fito daga Senegal kana 'yan shekarun baya ya samu takardar izinin zama dan Jamus har ma aka zabe shi a matsayin dan majalisar dokoki na daga cikin masu wannan ra'ayi to sai dai a wasu lokutan wasu masharta na ganin irin wannan fata na su Mr. Diaby ka iya cin karo da cikas domin kuwa ba kowacce jam'iyya ce ke bude kofofinta ga bakin da suka zama Jamusawa ba. Wannan ne ma ya sanya Camile Giousouf ta jam'iyyar CDU kana mai tushe da Turkiyya fatan kada irin wannan batu ya zaman wani abun maida hankali a zaben na Jamus na 24 ga wannan wata.