1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana ta taka rawa a sakin Mandela

Rahmatu Abubakar Mahmud GAT
February 11, 2020

Shekaru 30 bayan sako Nelson Mandela, al'ummar kasar Ghana na nuna farin ciki da kuma tunawa da rawar da kasarsu ta taka a fafutikar neman sakon Mandela da kawo karshen mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3XbJi
Angola - Nelson Mandela und Kofi Annan
Hoto: picture-alliance/AP/S. Kralj

A wannan Talata 11 ga watan Fabrairu ce ake bukin cika shekaru 30 da sakin tsohon shugaban Afirka ta Kudu, marigayi Nelson Mandela daga kurkuku bayan ya shafe shekaru 27 a sarka.

Mandela ya zama daya daga cikin shahararrun fursunonin siyasa na duniya, tare da jawo hankalin kasashen duniya game da yanayin bakake 'yan Afirka ta Kudu da ke zaune karkashin mulkin wariyar launin fata. Bayan an sake shi, an ba Mandela lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara 1993 kuma ya zama shugaban bakar fata na farko na Afirka ta Kudu a 1994. Da yake tsokaci kan yadda ya ji labarin sakin Mandela bayan zaman sarka na kimanin shekaru 27, Rev Emmanuel Borlabi masanin ilimin tarihi ya Ghana ya ce yi matukar farin ciki da sakin Mandela wanda yake kallo a matsayin jarumi inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

Friedensnobelpreis Mandela und de Klerk
Hoto: picture-alliance/AP Photo

 
"Lokacin ina sama da shekaru 30 ni kaina na yi farin ciki matuka domin babu wanda ya yi mafarki cewar za a saki Mandela cikin sauki. Nan take na yi tunanen kenan za a kawo karshen mulkin wariyar launin fata wanda hakan ya tabbata"
 
Ko wace irin rawa za a iya cewar Ghana ta taka wajen cimma burin saki Mandela? Ato kitoe wani dan jarida mai zaman kansa da ke da shekaru 16 lokacin sako Mandela daga Kurkuku:

Nelson Mandela 100 Jahre
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Hrusa


"Ghana ta taka muhimmiyar rawa wajen sako marigayi Mandela ta hanyar shirya tarurukan da kai kara a zauren taro na shugabanin duniya kamar Majalisar Dinkin Duniya da dai sauransu. Kuma a wannan zamanin shugaban jammiyyar ANC Oliver Thambo na da alaka sosai da Ghana, dalili kenan da ya sa marigayi Mandela ya kawo mana ziyara a lokkacin domin gode wa diyan kasar".
 
Mandela ya yi ritaya daga siyasa a shekara ta 1999, amma ya kasance mai samar da zaman lafiya da adalci tsakanin al'umma har zuwa mutuwarsa a cikin Disamba 2013.