1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwar baƙin haure na cikin haɗari

October 11, 2013

Ga alama har yanzu a kwai sauran aiki a gaban ƙungiyar haɗin kan Turai, wajen magance matsalar baƙin haure da ke fatan zuwa Turai ko ta wacce kafa.

https://p.dw.com/p/19yLa
Hoto: picture-alliance/ROPI

Wani jirgin ruwa da aka haƙikance yana ɗauke da bakin haure ya nutse a tekun Italiya a tsakanin Tsibirin Lampedusa da kuma Malta, mako guda bayan da wani jirgi makare da baƙin haure ya yi haɗari a Tsibirin na Lampedusa tare da haddasa mutuwar baƙin haure sama da 300. Rahotannin sun bayyana cewa tuni aka tura jami'an ceto da ba da agaji cikin ƙanana kwale-kwale da kuma jirage masu saukar Ungulu domin ceto mutanen da ke cikin jirgin da aka ƙiyasta cewa sun kai sama da 200.

Matsalar ta bakƙn haure dai tana ciwa ƙasashen nahiyar Turai tuwo a ƙwarya, inda cikin wannan mako ministocin cikin gida da ma 'yan majalisun ƙungiyar haɗin kan Turai EU, suka gudanar da tarurruka domin lalubo hanyar da za su bi ,su magance matsalar. Mafi akasari dai baƙin hauren na fitowa ne daga yankin Gabas ta Tsakiya da kuma nahiyar Afirka domin ƙauracewa rigingimun da ake fama da su a ƙasashensu da kuma tunanin zuwa Turai domin samun mafaka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourrahamane Hassane