1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwar 'yan gudun hijira a sassa na duniya

June 20, 2013

21 ga watan Yuni, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin nazarin halin da 'yan gudun hijira da aka tilastawa barin matsunnensu ke ciki, sakamakon dalilai na rigingimu.

https://p.dw.com/p/18ti1
:DW_Mali_Flüchtlinge4: Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 15. Mai 2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Déou, Burkina Faso
Hoto: DW/K. Gänsler

Nafisa Walet ta na zaune da 'ya'yanta mata guda uku, watau Neya da Halima da Tatu a karkashin wani babban Tanti. A gefe guda kuwa an shimfida katifa da abun rufa. A wani lungu kuwa kayayyakin girki ne ke jibge. 'Yan matan guda uku kuwa suna wasan charafke da duwatsu tare da waka. Tun daga farkon shekara ta 2012 nedai, wadannan Iyalai suka je gudun hijira a Mentao ta kudu, da ke kasancewa daya daga cikin sansanoni 11 na 'yan gudun hijira a kasar Burkina faso, da ke makwabtaka da Mali daga kudanci. Iyalin Nafisa dai na zama daya ne daga cikin 'yan gudun hijira kimanin 174.100, da suka tsere daga Mali tun bayan barkewar rikicin 'yan tawayen Abzinawa a watan Janairun shekarar da ta gabata.

Shekara guda da rabi bayan barin matsugunnen nasu dai, Nafisa da 'ya'yanta na fatan ganin cewar sun koma yankinsu na asali.

Ta ce" idan da za'a iya cimma daidaituwa tsakanin gwamnatin Mali da masu fafatukar neman 'yancin cin gashin kan na yankin Azawad, da da wannan maraice zamu iya barin wannan wurin zuwa giidajenmu". A ganinta dai da don ita ce, da an bar yankin arewacin Malin ya samu 'yancinsa, kamar yadda da yawa daga cikin 'yan kibilar ta Abzinawa ke fata.

Tuareg-Flüchtlinge spielen Karten, um sich die Zeit zu vertreiben; 19. März 2013, Djibo (Burkina Faso); Copyright: DW/K. Gänsler
Abzinawa 'yan gudun hijiraHoto: DW/K. Gänsler

Wannan hira da aka yi da Nafisa Walet dai, an yi shi ne watanni biyu da suka gabata, sai dai babu alamun cewar burinsu ya cika na ganin cewar sun koma gidansu na asali a yankin arewacin Mali. Kungiyar 'yan tawayen abzinawa ta MNLA da majalisar neman hadewar yankin Azawad dai, za su iya cimma wananna muradu na al'ummar yankin ne bayan zazzafara tattaunawa da gwamnati kasar ta Mali, na ganin cewar an gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Yuli a birnin Kidal. Kidal dai na karkashin ikon 'yan tawayen MNLA.

Har yanzu dai akwai sauran tafiya a kokarin warware rikicin yankin arewacin Mali. Kana ba'a daraja wa hakkin bil'ama, a cewar kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch. Duk da cewar sojojin Fransa da na kungiyar ECOWAS sun ci karfin 'yan tawayen, babu tabbas dangane da yiwuwar samar da zaman lafiya da ake muradi a wannan yanki, kamar yadda direktan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Karl Steinacker ya bayyana.

" Ba ma la'akari da 'yan gudun hijira dake komowa. Amma babu alamun lamura sun ingantu a yankin arewacin Mali. Dangane da maganar tsaro kuwa, ba za'a iya cewar babu kungiyoyin da ke dauke da makamai ba. Kazalika su ma sojojin Malin dole ne su kasance a karkashin sa idon sojojin ketare domin gudun cin zarafin mutane".

Titel: DW_Mali_Flüchtlinge 2: Schlagworte: Binnenflüchtlinge, Sévaré, UNCHR, Mali Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 16. Dezember 2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Sévaré, Mali DW_Mali_Flüchtlinge2: Fatouma Arbi weiß nicht, wie sie ihre Familie durchbringen soll
'Yan gudun hijirar Mali a kasar Burkina fasoHoto: DW/K. Gänsler

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta kiyasta cewar kashi 80 daga cikin 100 Abzinawa dai suna gudun hijira ne a kasashen da ke makwabtaka da Mali. A yayin da sauran kabilu kamar Foula da Songhai da yawansu ya kai dubu 300, sun nemi mafaka ne a cikin Mali. Aisha Yattara na daya daga cikinsu. A kan cinyarta akwai jariri mai watanni biyu yana da rusa kuka.

" Yaron bashi da lafiya. Sai dai bamu da da kudi, balle a yi mishi allura. Kan haka ne mu ke zaune a gida. Muna jiran yayarsa ne watakila ta kawo kudi, sai mu kai shi wajen likita domin a duba shi. A nan ba mu da likita".

Bayan matsalar magunguna, 'yan gudun hijirar na fuskantar matsalar rashin ingantaccen abinci, domin basu da wani zabi, sai dai zaman lafiya, ya fi zama dan sarki.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh