1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwar yara na cikin hadari a Afirka

Nasir Salisu Zango GAT
November 20, 2018

Yayin da ake bikin ranar yara ta duniya, kananan yara a Najeriya na cikin garari a jihar Kano da ke arewacin kasar inda yawaitar tallace-tallace da ayyukan karfi ke barazana ga rayuwa da makomar kananan yaran.

https://p.dw.com/p/38c5a
Bettelnde Kinder in Dutse, Nigeria
Hoto: DW/Z. Rabo Ringim

Baya ga batun tallace-tallace da ayyukan karfi kananan yara na fuskantar azabtarwa ko dai daga kishiyoyin uwa ko kuma abokan zama, lamarin da ke kara barazana ga zamantakewar alummar yankin na arewacin Najeriya.

Kukan wata kankanuwar yarinya kenan wacce bata wuce shekara biyu ba a duniya, wacce faccalar mahaifiyar ta wato matar kawunta ta tsoma mata hannuwa biyu a cikin tukunyar shinkafa dake zabalbala wacce ta babbake mata hannaye duka biyun suka kuma zagwanye,irin wannan azabatrwa kadan ce daga cikin irin matsalolin da yara ke fuskanta a arewacin Nigeria,wanda kuma ke cigaba da barazana ga zamantakewar alumma a yankin.

Nigeria - Irewha Hunt Festival
Hoto: picture-alliance/AA/H. Chukwuede

Fatima Bala mahaifiyar wata karamar yarinya ce 'yar kimanin shekaru biyu da ake shirin yi wa aiki a asibitin kasa ta Dala da ke a birnin Kano wacce matar kawunta ta tsoma mata hannuwa biyu a cikin tukunyar shinkafa a saman wuta da suka zagwanye, ta kuma bayyana cewa wata biyar kenan ana kokarin yin aikin amma har yanzu hannun bai daina zubar jinni ba.

Bincike ya kuma nuna cewar daruruwan kananan yara ne ba sa zuwa makaranta a arewacin Najeriya, wadanda galiban suna kan hanya suna gararamba, yayin da wasu ke yawon jari bola wasu kuma na tallace-tallace ko kuma aikin karfi.

To amma duk da haka akwai wasu yaran da iyayensu ke da sukuni suka kuma ba su ilimi, har wasu daga cikinsu ke bayyana irin burinsu idan sun girma da kuma nuna damuwarsu a kan yadda wasu 'yan uwan nasu yara ke tallace-tallace.


Shekh Ibrahim Khalil babban malami ne mai wa azi a jihar Kano, ya ce cin zarafin kananan yara yakan bata musu tunani tare da tasiri a rayuwarsu har abada. Dangane da masu gararamba wadanda ba sa zuwa makaranta kuma shek Ibrahim Khalil ya ce babbar barazana sukan iya zama a cikin alumma.

Nigeria | Kinder in Maidugri
Hoto: DW/T. Mösch

Duk da cewar yau ne ake bikin ranar yara ta duniya masana da sauran jama'a na kira ga hukumomi da su inganta karatu a makarantun gwamnati inda nan ne 'ya'yan talakawa za su iya zuwa domin neman ilimi, don kauce wa haihuwar da marar idanu a nan gaba.