1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice ta jaddada matakin Amurka na taimakawa palasdinawa

October 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuhM

Sakatariyar harkokin wajen Amurka CR tace karin tallafi na kayayyakin agaji ga yankin Palasdinawa da kuma walwalar shigi da fici a tsakanin ta da Israela, abubuwa ne da zasu taimaka wajen inganta rayuwar mutanen yankin.

Rice ta fadi hakan ne kuwa jim kadan bayan wata tattaunawa da tayi ta ido da ido da shugaban yankin Mahmud Abbas.

Duk da cewa sakatariyar harkokin wajen ta Amurka bata yi alkawarin bawa yankin na Palasdinawa tallafin raya kasa ba a madadin kasar ta , bayanai sun nunar da cewa, akwai yunkuri da Amurkan keyi na ganin kayayyakin agaji na ci gaba da isa yankin.

A kuwa yayin da yankin na Palasdinawa ke kokarin shawo kann rikicin da aka kwashe watanni tara ana yi, a dai dai lokacin ne kuma dakarun Israela suka kai wani hari a zirin gaza, wanda yayi sanadiyyar rasuwar yan kungiyyar Jihadil Islami guda biyu.

A cewar dakarun na Israela, sun halaka mutane biyun ne, bisa zargin su na shirya kai harin ta´addanci izuwa kasar.