1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rijiyar man Oloibiri mai dadadden tarihi

March 26, 2014

Rijiyar man Oloibiri ce inda aka fara gano danyen mai a Afirka, yanzu rijiyar ta kafe kuma duk da alkawarin da ta yi, gwamnati ba ta ba ta martabar da ya kamace ta ba

https://p.dw.com/p/1BW3u
Nigeria - Oloibiri Öl-Quelle
Hoto: DW/ Haussa

Garin Oloibiri dake karamar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, gari ne mai tattare da tarihi mai girma, bisa la'akari da cewar, a nan ne aka fara gano rijiyar danyen mai ba ma a Najeriya kawai ba, har ma a daukacin Afrika.

To sai dai, ko da yake al'ummomin garin da wannan rijiya ta mai take suna korafin kuskuran tarihi na wannan rijiya, wani karin korafin kuma shi ne yadda babu wani abin arziki ga iyalan dake da mallakin filin da rijiyar ta mai take, da ma daukacin garin da al'ummarta.

Shekaru hamsin da shida kenan yanzu da samun man a yau, bayan da aka yi ta gararambar neman gano inda danyan man yake a Najeriya.

Daga ka bar Owerri babban birnin jihar Imo dake yankin gabashin Najeriya za ka fada yankin Yenagoa da kewaye, dake jihar Bayelsa wanda kuma shi ne babban birnin jihar a yau, kuma nan ne aka gano rijiyar mai ta farko, a wani gari mai suna Oloibiri. Shi dai wannan garin ya na da nisan Kilomita kusan dari da ashirin daga birnin na Yenagoa.

Nigeria - Oloibiri Öl-Quelle
Chief Cleopas Iburu AmakuroHoto: DW/ Haussa

Takaddama kan yankin da Oloibiri yake a zahiri

Sai dai kuma al'ummar wani gari da ake kira Otabage, wanda taki kadan ne daga inda wannan rijiya ta mai ta ke, sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda tarihi ya dauka cewar Oloibiri ne garin da rijiyar take, ba garin Otabage ba, bayan kuma garin na Otabage ne inda wannan rijiyar take.

Dan haka ma wani da ake kira Chief Cleopas Iburu Amakuro, dake zaman babba a tsatsan iyalin Idaomuno, a garin al'ummar Otabage, wadda kuma su ne da mallakin filin da wannan rijiya take, ya bayyana cewar.

Nigeria - Oloibiri Öl-Quelle
Allulan dake nuna hanyar zuwa ganin rijiyar man OloibiriHoto: DW/ Haussa

"A yanzu dai ko da yake sunan Oloibiri ba zai kankaru ba, to amma dai za mu so a rika kiran wannan guri da rijiyar take rijiyar mai ta farko ta Oloibiri a Otabage. Kasan tun shekara ta 1956 aka gano wannan rijiya, ba kuma gaya min akai ba, na gani Idanuna sarai".

Ko da yake da farko zan iya cewar mutanen Oloibiri sun dan ci arzikin wannan rijiya, sai dai al'ammura sun sauya, bayan yakin basasar Najeriya.

Rijiyar man Oloibiri ba ta sauya rayuwar al'ummomin ba

"Tun daga wannan lokaci kuma babu sauyi a rayuwarmu, don mun yi fafutuka har mun gaza, sai wahalhalun rashin ababen more rayuwa a iyalinmu da al'ummar Otabage inda a nan rijiyar ta mai take."

Akwai dai koke-koken rashin kulawa ga alummar ta Oloibirin Otabage, duk kuwa da daukakar da suka samu ta gano mai a garin nasu a tashin farko. Ga Wata Madam Ross Enemia yar garin, da kuma ta ji hausa kadan.

Nigeria - Oloibiri Öl-Quelle
Ross Enemia (Hagu) da Ezibanye IyeHoto: DW/ Haussa

"Tun lokacin da na taso a garin nan, ina sane da cewar an gano danyan mai, sai dai kuma wannan alheri bai sa rayuwarmu ta sauya ba, domin har yanzu ba mu da wata makarantar kirki, wahala kawai muke sha, yaranmu da kan gama Makaranta, kan zauna ba aikin yi."

Yayin dai da na isa inda harabar wannan rijiya take, na ga a kewaye take da waya, da na shiga ciki daf da inda kan rijiyar take, na ganta a bushe, alamar cewar man rijiyar ya kafe, sai dai tarihin.

Gwamnatin Tarayya ba ta cika alkawuranta ba

Sannan bayanin da na samu, shi ne cewar, gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin kyautata harabar da rijiyar take don masu ziyarar gani da Ido dan tarihi. To sai dai fa shekaru da dama ake wannan batu, kuma har kawo yanzu babu wani katabus da aka yi.

Da dama dai al'ummomi a yankin Niger Delta dake makwabtar inda ake aikin danyan mai, kan koka cewar yanayin bai haifar musu da komai ba sai gararin gurbatar yanayi da muhalli, da kuma hakan ya durkusar da rayuwarsu, ba tare da kulawar Hukumomi ko Kamfanonin mai ba a kasar.

Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Pinado Abdu Waba