1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a yankunan Falasdinawa ya yi sanadin mutuwar mutum 4

June 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuvQ
An sake gwabza fada a Zirin Gaza tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna wato Hamas da Fatah. Majiyoyi daga hukumomin tsaro sun yi nuni da cewa akalla mutane 4 aka halaka cikin su har da wata mata mai juna biyu. An dai shafe makonni da dama ana dauki ba dadi tsakanin kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da kungiyar Hamas mai jan ragamar gwamnati. Bangarorin biyu na fafatawa ne don rike madafun iko na hukumomin tsaron Falasdinu. A wani labarin kuma a karon farko cikin watanni 3 gwamnatin Hamas ta biya albashin ma´aikatan hukumar mulkin cikin gashin kai na wata daya. Rahotanni sun nuna cewa ma´aikata dubu 10 daga cikin dubu 165 suka samu albashin nasu na wata daya-daya. Tun bayan darewarta ka karagar mulki, gwamnatin Hamas ke fuskantar matsalar karancin kudi bayan da kasashen yamma suka daina turawa hukumar mulkin Falasdinu da kudaden taimako.